Arewa Ta Dare Gida 2 kan Zaben Tinubu a 2027, Shugabannin Siyasa Sun Ja Layi

Arewa Ta Dare Gida 2 kan Zaben Tinubu a 2027, Shugabannin Siyasa Sun Ja Layi

  • Shugabannin Arewa sun rabu kan yiwuwar sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027, yayin da wasu ke goyon bayansa, wasu kuma na adawa
  • Wasu na zargin gwamnatin Tinubu da rashin cika alkawura a yankin da kawo talauci, yayin da wasu na yaba ci gaban da suka samu karkashin mulkinsa
  • Manyan kungiyoyin Arewa da dama sun bayyana matsayinsu kan batun, suna nuna rashin hadin kai game da sake zaben Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugabannin Arewa sun dare gida biyu kan yiwuwar sake zaben Bola Tinubu a shekarar 2027.

Masana suka ce wannan kusan shi ne karon farko da aka samu haka inda mafi yawanci Arewa ke dunkulewa kan dan takara da ke ba su damar darewa mulki.

Kara karanta wannan

'Kafin rana ya fadi': Malamin Musulunci ya fadi 'dalilan' da za su ka da Tinubu a zaben 2027

Yadda take neman kwayewa Tinubu a zaben 2027
Arewa ta kasu kashi-kashi game da sake zaben Bola Tinubu a zaben 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yadda Arewa ta rabu kan zaben Tinubu a 2027

Rahoton PUNCH ya nuna cewa tsohuwar hadin kan Arewa ta rabu gida biyu musamman kan zaben Tinubu da ake tababa a kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin manyan shugabannin Arewa na son ganin Tinubu ya sauka a 2027, yayin da wasu 'yan tsiraru ke goyon bayan sake zabensa.

Wasu na zargin Tinubu da rashin nuna damuwa ga yankin Arewa, suna kuma korafi kan matsin tattalin arziki da talauci da ya addabi yankin.

Duk da haka, wasu 'yan tsiraru daga yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya da wasu na Arewa na jaddada cewa sun samu ci gaba karkashin mulkinsa.

Sun bayyana goyon bayansu bisa la’akari da ayyukan raya kasa da kuma nade-naden mukamai.

2027: Yan siyasa da kungiyoyi sun fadi matsayarsu

Manyan kungiyoyin Arewa kamar Arewa Consultative Forum da League of Northern Democrats sun bayyana matsayinsu kan batun.

Kara karanta wannan

Shugabannin Arewa sun yiwa Ganduje kaca kaca, sun kalubalanci tazarcen Tinubu

Wasu sun sha alwashin marawa dan takara daban baya, yayin da wasu ke cewa ba za su bari a tilasta musu zabin Tinubu ba.

Rashin jituwa a tsakanin shugabannin Arewa ya fito fili, duba da musayar ra'ayi tsakanin Nasir El-Rufai da Sanata Shehu Sani kan yadda Tinubu ke tafiyar da al'amuran tsaro da cigaban yankin.

Dan APC ya fadi ra'ayinsa ga Legit Hausa

Wani dan a mutun APC a Gombe, Muhammad Ibrahim ya ce tabbas akwai matsaloli a jam'iyyar amma tana kan turba mai kyau.

Ibrahim ya bayyana irin kalubale da suke fuskanta wanda duk bai wuce hassada ce ta yan PDP ba.

"Ba za mu ce babu matsaloli ba musamman tsadar rayuwa amma yan adawa ke kara ruruta lamarin saboda jawo mana bakin jini."

- Ibrahim Muhammad

Duk da haka, Ibrahim ya shawarci shugabanni musamman na APC su rika kula da inganta rayuwar al'umma domin rage radadin da ake ciki.

Kara karanta wannan

'Arewa ba za ta yafe ba': An fadi yadda Tinubu zai lallabi yankin a zaben 2027

Babachir ya gargadi Tinubu kan zaben 2027

Mun ba ku labarin cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya a mulin Muhammadu Buhari, Babachir Lawal ya magantu kan zaben 2027.

Babachir ya ce idan Tinubu bai sasanta da Arewa ba, zai fuskanci barazanar rashin nasara a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel