'Wasu 'Yan APC Sun Fara Hada Kai da 'Yan Adawa domin Hamayya da Tinubu a 2027'
- Wata ungiyar magoya bayan Bola Tinubu ta ce babu jam’iyyar adawa da za ta iya kayar da shi a lokacin da zai nemi tazarce
- Shugabannin kungiyar sun gargadi ‘yan adawar da ke taruwa ba su da karfin cire Bola Tinubu daga mulkin Najeriya
- Kungiyar DOJ ta tono shirin wasu 'yan APC da ke hada kai da 'yan adawa domin hamayya ga Tinubu a zabe mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar magoya bayan Bola Ahmed Tinubu ta DOJ ta bayyana cewa babu wata jam’iyyar adawa da za ta iya hana APC nasara a zaben shugaban kasa na 2027.
Shugaban kungiyar ta kasa, Abdulhakeem Adegoke Alawuje ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, inda ya ce duk wata hadakar ‘yan adawa ba za ta yi nasara kan Tinubu ba.

Asali: Facebook
Jaridar the Nation ta rahoto cewa Abdulhakeem Adegoke Alawuje ya ce ya kamata 'yan adawa su je wajen Tinubu koyon siyasa maimakon kokarin kayar da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DOJ: 'Babu mai iya kayar da Bola Tinubu'
A cewar kungiyar DOJ, yunkurin wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na hada kai don kayar da Tinubu ba zai yi tasiri ba domin ba su da karfin yin hakan.
Jungiyar DOJ ta ce:
“Gamayyar ‘yan siyasar da ba su da karko, kuma marasa wata kaifin akida, ba za su iya kawar da Tinubu ba a 2027.
"Wadanda ke jagorantar wannan sabon gungu ba su da wata damuwa da ci gaban kasa, illa son zuciya da burin kansu.”
Batun 'yan APC na hada kai da 'yan adawa
Kungiyar ta ce yayin da wasu manyan ‘yan adawa ke yakar gwamnatin Tinubu saboda sauye-sauyen da yake aiwatarwa, wasu ‘yan APC masu son zuciya na kokarin hada kai da ‘yan adawa.

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa Tinubu zai ci zaben 2027': Kwankwaso ya magantu, ya tabo maganar Ganduje
DOJ ta ce 'yan adawa masu kokarin kafa sabuwar hamayya ga Bola Tinubu ba za su yi nasara ba a zabe mai zuwa.
Kungiyar DOJ ta fara kamfen tun 2023
Shugaban kungiyar ya yi gargadi da cewa idan ‘yan adawa na tunanin za su iya maimaita irin salon da aka yi a 2015, inda PDP ta sha kashi hannun APC, to sun yi kuskure.
Alawuje ya ce:
“Ya kamata su tuna cewa Tinubu ne babban jagoran nasarar 2015, kuma a yanzu shi ne shugaban kasa.
"Ba su da karfin tunkarar Jagaban Borgu, wanda ya lashe zaben 2023 duk da kalubalen da ya fuskanta.”
DOJ ta ce ta riga ta fara yakin neman zaben Tinubu tun daga 2023, don haka ta bukaci duk wani mai rike da mukami ko wanda bai samu mukami ba a gwamnati da su goyi bayan Tinubu.
Alawuje ya ce:
“Muna kallon wannan sabuwar hamayya a matsayin bata lokaci da wofintar da kudade.
Abin takaici ne cewa daga cikin su akwai ‘yan APC da ba za su iya zama ba tare da mukamin gwamnati ba.”
Ya kawo misali da Tinubu, ya ce ya kwashe shekaru 16 ba tare da rike mukami ba, amma bai taba yin tawaye ko kokarin rushe jam’iyyarsa ba.
Dr. Bugaje ya ragargaji Buhari da Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Dr Usman Bugaje ya ce mulkin APC bai tsinana komai ga Najeriya da 'yan kasa ba.
Dr Bugaje wanda ya kasance tsohon jigo a APC ya ce mulkin shugaba Muhammadu Buhari da Bola Tinubu sun kara jefa Najeriya a matsala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng