Tinubu: 'Dan Majalisa Ya Hada Ganduje da El Rufa'i, Ya Gyara Musu Zama kan 2027
- 'Dan majalisar wakilai, Hon. Aminu Jaji, ya ce an yi gaggawa da wasu 'yan siyasa suka fara tayar da jijiyar wuya kan zaɓen 2027
- Ya yi bayanin ne a wurin kaddamar da shirin hadin kai da Ƙungiyar Tsofaffin Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta shirya a Abuja
- Rikici ya ƙara tsananta tsakanin wasu manyan ‘yan siyasa da ke cewa ana cutar da Arewa, yayin da Abdullahi Ganduje bai tare da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Dan majalisar wakilai daga Jihar Zamfara, Aminu Jaji, ya gargadi tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje kan 2027.
Hon. Aminu Jaji ya bukaci jagororin jam'iyyar APC da su daina tada rikici kan zaɓen 2027, yana mai cewa lokaci bai yi ba.

Asali: Twitter
Punch ta wallafa cewa Aminu Jaji ya bayyana hakan ne a wurin taron kaddamar da shirin hadin kai da Ƙungiyar Tsofaffin Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta shirya a Abuja a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Magana kan wa’adin Bola Tinubu na 2
A ‘yan makonnin nan, matsin lamba ya ƙaru daga wasu shugabannin Arewa kamar Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, da wasu kungiyoyi da ke adawa da mulkin Bola Ahmed Tinubu.
Ganduje ya ƙara rura wutar rikicin bayan ya ce duk wani ɗan siyasar Arewa da ke neman takara a 2027 ya janye tunanin.
Shugaban APC ya ce:
"Idan har wani daga Arewa ya gama wa’adinsa na shekaru takwas ba tare da katsalandan ba, to bai dace a hana Tinubu damar kammala wa'adinsa ba."
Wasu 'yan siyasar Arewa sun koka kan cewa dangantaka tsakanin Tinubu da Arewa na ta yin tsami.

Kara karanta wannan
'Komai ya wuce': El Rufai ya fadi manyan dalilai 3 na tallata Tinubu a zaben 2023
Wasu masu sharhi na ganin idan aka ci gaba da haka, nan gaba Arewa za ta yi masa irin abin da aka yi wa Goodluck Jonathan a 2015.
A wani bangaren, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi wasu maganganu da suke nuna adawa da gwamnatin Bola Tinubu.
Jaji ya bukaci a hakura da maganar 2027
Hon. Jaji ya nuna rashin jin daɗinsa da yadda wasu ke fara kamfen na 2027 tun da mulkin Tinubu bai cika shekaru biyu ba.
Dan majalisar ya ce:
"Na fahimci cewa El-Rufai na fargabar 2027 saboda irin manufofin da wannan gwamnati ke aiwatarwa.
"Wataƙila kuma yana kallon yadda ‘yan adawa ke shirin 2027. Amma har yanzu maganar 2027 ba ta zo ba."
Hon. Jaji ya yi kira ga ‘yan siyasa su sanya kishin kasa a gaba, yana mai cewa:
"Ya zama wajibi mu daina siyasar raba kai. Wannan ƙasar tamu tana cikin mawuyacin hali, kuma abin da muke buƙata shi ne haɗin kai, ba rigima ba."

Kara karanta wannan
"Najeriya ta yi Rashi," Tinubu ya kaɗu da Allah ya yi wa fitaccen malamin Musulunci rasuwa
2027: ACF ta gargadi Ganduje kan Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa ACF ta gargadi shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje kan maganar zaben 2027.
Kungiyar ACF ta ce bai kamata Abdullahi Ganduje ya ce 'yan Arewa su hakura da maganar takara ba a 2027 saboda tazarcen Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng