Rikicin APC Ya Fito Fili, Shugabanni na Harbin Juna da Bakaken Maganganu

Rikicin APC Ya Fito Fili, Shugabanni na Harbin Juna da Bakaken Maganganu

  • Rikicin shugabanci a APC reshen jihar Benue ya sake kunno kai yayin da Austin Agada ya halarci taron jam’iyya a Abuja
  • Shugaban kwamitin rikon kwaryar da aka nada, Benjamin Omale ya soki Agada yana mai cewa ba shi ne sahihin shugaban jam'iyyar ba
  • Agada ya maida martani, yana mai cewa shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar a Benue, kuma an gayyace shi taron Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Rikicin jam’iyyar APC reshen jihar Benue ya sake kamari bayan bayyanar tsohon shugaban jam’iyyar, Austin Agada, a wani taro na kasa da aka gudanar a Abuja.

A taron, shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya kasance tare da wasu manya kuma jiga-jigan jam’iyyar.

Ganduje
Rikicin APC ya kara kamari a jihar Benue. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa shugaban kwamitin rikon kwarya na APC a Benue, Dr Benjamin Omale, ya fito da wata sanarwa inda ya zargi Agada da kutse cikin taron don neman suna.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta dare gida 2, sabon rikici ya mamaye manyan 'yan adawar Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omale ya bayyana Agada a matsayin wanda ke kokarin daukar hotuna da shugabannin APC don nuna cewa yana da sahalewar jam’iyyar.

Yadda aka fara rikicin APC a Benue

Ana fama da rikicin shugabanci a APC a jihar Benue ne tsakanin bangaren gwamnan jihar, Hyacinth Alia, da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume.

A dalilin hakan, shugabancin APC na kasa ya rushe kwamitin Agada tare da nada Omale a matsayin shugaban rikon kwarya.

Agada ya kalubalanci matakin da shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya dauka a kotu, inda kotun jihar Benue ta maido da shi matsayin shugaban APC na jihar.

Omale ya soki Agada kan taron Abuja

Shugaban kwamitin rikon kwarya, Benjamin Omale, ya yi zargin cewa Agada yana kokarin yaudarar jama’a da hotuna marasa tushe.

“Austin Agada yanzu yana neman inda Ganduje yake, yana tsayawa a bayansa don daukar hoto, sannan yana barin wurin nan take,”

Kara karanta wannan

"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027

- Benjamin Omale

Omale ya bayyana cewa tun bayan rushe Agada, kwamitin rikon kwarya ne ke tafiyar da jam’iyyar a jihar.

Ya ce tun bayan sauya shugabanci, APC ta samu gagarumar nasara a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a ranar 5 ga Oktoba, 2024.

Agada ya musanta zarge-zargen Omale

A martaninsa, Austin Agada ya ce shi ne halastaccen shugaban APC a Benue, kuma an gayyace shi taron Abuja.

“Babu shakka, an gayyace ni taron kuma na halarta a matsayina na shugaban jam’iyya na jihar,”

- Austin Agada

Sakataren yada labarai na bangaren Agada, Daniel Ihomun, ya ce kalaman Omale ba su da tushe balle makama.

“Wannan wani yunkuri ne kawai na bata sunan Agada da kuma rage masa kima,”

- Daniel Ihomun

Ana zuba ido domin ganin ko shugabancin jam’iyyar APC na kasa zai dauki mataki game da halin da ake ciki domin warware rikicin da ya addabi jam'iyyar a jihar.

Kara karanta wannan

An taso gwamna a gaba kan nada tsohon shugaban APC ya jagoranci hukumar zabe

ACF ta gargadi shugaban APC kan 2027

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar ACF ta gargadi shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje kan zaben 2027.

ACF ta ce maganar Abdullahi Ganduje kan cewa 'yan Arewa su hakura da takara a 2027 har sai Bola Tinubu ya kammala wa'adi na biyu ba ta da tushe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng