Ana Fargabar Lafiyar Mataimakin Gwamna da babu Labarinsa na Tsawon Watanni 3

Ana Fargabar Lafiyar Mataimakin Gwamna da babu Labarinsa na Tsawon Watanni 3

  • Mutane sun fara shiga cikin damuwa a jihar Taraba kan rashin ganin Mataimakin Gwamna, Aminu Alkali na tsawon lokaci
  • Ana fargabar Aminu Alkali bai bayyana a bainar jama'a ba har na tsawon kwanaki 90 kenan, kuma ba a yi wa jama'a bayani ba
  • Rahotanni na cewa Alkari na fama da mummunan hawan jini kuma ana jinya a asibiti tun fiye da watanni biyu da suka wuce a Abuja
  • Jama'a da lauyoyi sun bukaci Gwamna Agbu Kefas da majalisa su bayyana gaskiyar lamari domin kare dokar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jalingo, Taraba - Ana cikin fargaba a Jihar Taraba kan rashin bayyanar mataimakin Gwamna, Alhaji Aminu Alkali.

Ana hasashen Aminu Alkali bai yin ayyukan ofis tsawon kwanaki 90 kenan wanda hakan ya jefa shakku game da lafiyarsa.

Kara karanta wannan

'Suna jawo bala'i': Basarake ya haramta ayyukan bokaye mata bayan kisan dan majalisa

An bukaci bincike kan lafiyar mataimakin gwamna a Taraba
Al'umma a jihar Taraba na neman sanin halin da mataimakin gwamna ke ciki. Hoto: Agbu Kefas.
Asali: Facebook

An kokwanto kan lafiyar mataimakin gwamna Kefas

Rahoton Leadership ya tabbatar cewa tun daga ranar 11 ga Nuwambar 2024, ba a ji duriyarsa ba, ciki da wajen jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamarin ya jawo shakku da tunawa da abin da ya faru da tsohon gwamna, marigayi Danbaba Suntai.

Rahotanni sun ce Alkari na fama da matsalar bugun zuciya kuma ana jinyarsa asibiti a Abuja tun fiye da watanni biyu da suka gabata

Jama'ar jihar na kira ga Gwamna Agbu Kefas ya bayyana gaskiya kan rashin ganin mataimakin gwamna tare da daukar matakin gaggawa kan lamarin.

Haka kuma, sun bukaci Majalisar Dokoki ta jihar ta cika aikinta na doka domin tabbatar da cewa ba a tauye hakkin jama'a ba.

Lauya ya bukaci fito da gaskiya kan lamarin

Lauyan kare hakkin bil'adama, Barista, Bilyaminu Maihanchi, ya rubuta wasika ga gwamna da Majalisar Dokoki don amfani da kundin tsarin mulki sashe na 189.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

A wasikar, ya bukaci a yi bincike kan rashin mataimakin gwamnan da daukar mataki na doka da zai fayyace gaskiyar lamari.

Ya kuma yi kira ga al'ummar Taraba su dage wajen neman bayanin gaskiya daga shugabanninsu tare da tabbatar da adalci a mulki.

Musabaka: Gwamna Kefas ya taya matashi murna

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas na Taraba ya yi farin ciki da Hafeez Mujaheed Salihu ya lashe gasar musabaka ta kasa da aka yi.

An yi gasar a Kano wanda kungiyar Izalah bangaren Jos ta gudanar inda gwamnan ya ce nasarar Mujaheed na da nasaba da jajircewarsa a addini.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.