Gaskiya Ta Fito da Ake Raɗe Raɗin Shugaban AfDB na Shirin Kawo Wa Tinubu Cikas a 2027
- Shugaban bankin raya Afirka watau AfDB ya musanta rahotannin da ake yaɗa wa cewa yana da niyyar neman takarar shugaban ƙasa a 2027
- Akinwumi Adesina ya ce kafafen watsa labarai da sauran jama'a sun yi wa maganarsa gurguwar fahimta domin ba haka yake nufi ba
- Tun farko dai an fara yaɗa rahotannin takarar Adesina ne bayan wata hira da aka yi da shi, inda aka ji yana cewa a shirye yake ya ba da gudummuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban bankin raya nahiyar Afirka (AfDB) mai barin gado, Akinwumi Adesina, ya karyata rahotannin da ke danganta shi da takarar shugabancin Najeriya a 2027.
An yaɗa jita-jita a kafofin sada zumunta da na yaɗa labarai cewa shugaban AfDB ya fara hangen kujera lamba ɗaya a Najeriya.

Asali: Twitter
Raɗe-raɗin ya bazu ne bayan wata hira da aka yi da shi a Arise TV, inda aka ji yana cewa a shirye yake ya ba da gudummuwa a ƙasarsa Najeriya, Afirka ko a duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman da Adeshina ya faɗa da farko
A lokacin da aka tambaye shi ko yana da niyyar yin takara bayan karewar wa’adinsa a bankin AfDB, Adesina ya ce:
"Zan zauna a shirye domin ba da gudummuwa a kowace irin dama na samu, a duniya, a Afirka, ko a ƙasata Najeriya."
Wannan amsa da ya bayar ne mutane suka fassara ta da cewa yana burin neman zama shugaban Najeriya a zaɓen 2027 mai zuwa.
"Ban ce zan yi takara ba" – Adesina
Sai dai a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 13 ga Fabrairu, 2025, Adesina ya bayyana cewa an yi wa maganarsa mummunar fassara.
Ya ce ko kaɗan ba shi da burin neman kujerar shugaban ƙasa a Najeriya bayan ƙarewar wa'adinsa a bankin AfDB.

Kara karanta wannan
"Tinubu zai sha wahala": LP ta bayyana wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a 2027
Akinwumi Adesina ya ce:
"An fassara wani ɓangare na hirar da na yi a @ARISEtv ba daidai ba, ni ba haka nake nufi ɓa kuma wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun sake yaɗa maganar da fassarar da ba haka nake nufi ba
"Abin da na faɗa shi ne, zan kasance a shirye domin yin hidima a kowace irin dama da na samu, a duniya, a Afirka, ko a ƙasata Najeriya.’"
"Babu wurin da na ce zan nemi takarar zama shugaban kasa a Najeriya, ba haka nake nufi ba."
Adesina ya ƙara da cewa duk wanda ya saurari cikakkiyar hirar zai fahimci cewa babu wurin da ya nuna cewa yana da niyyar yin takara.
LP ta faɗi wanda za ta ba takarar 2027
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar LP ta fara shirye-shirye gadan-gadan na tunkarar zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa a shekarar 2027.
Mai magana da yawun LP na kasa ya ba da satar masa kan wanda za su ba tikitin takara a 2027 ta yadda Bola Tinubu zai gamu da ƙalubaƙe babba a zaɓe na gaba.
Asali: Legit.ng