2027: Ganduje Ya Sha Rubdugu da Ya Fara Tallata Tinubu ga 'Yan Arewa

2027: Ganduje Ya Sha Rubdugu da Ya Fara Tallata Tinubu ga 'Yan Arewa

  • Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) da wasu manyan ‘yan siyasar Arewa sun ce ba za a tilasta wa yankin sake zabar Tinubu ba a 2027
  • Kungiyar ta ce babu wanda zai iya magana da yawun daukacin ‘yan Arewa, don haka kalaman shugaban APC, Abdullahi Ganduje ba su dace ba
  • Ganduje ya ce dole ne 'yan Arewa su jira shugaba Bola Tinubu ya kammala wa'adi na biyu kafin mulkin Najeriya ya dawo Arewacin kasar
  • Sai dai kungiyar ACF ta jaddada cewa ‘yancin masu kada kuri’a ne su yanke hukunci kan wanda za su zaba ba tare da an tilasta musu zaben wani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar (ACF) da wasu ‘yan siyasar Arewa sun yi Allah-wadai da kalaman shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, kan batun takara a 2027.

Kara karanta wannan

Arewa: El-Rufa'i ya aika gargadi ga APC da Tinubu kan zaben 2027

Abdullahi Ganduje ya bukaci ‘yan siyasar Arewa da ke da burin takarar shugabancin kasa a 2027 su janye, yana mai cewa dole ne a ba Tinubu damar kammala wa’adin mulki na biyu.

Ganduje
ACF ta yi martani ga Ganduje kan takarar Tinubu a 2027. Hoto: Salihu Tanko Yakasai|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ACF da wasu manyan ‘yan Arewa sun bayyana cewa babu wanda zai tilasta wa yankin zaben Tinubu a 2027, don haka kalaman Ganduje ba su dace ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Ganduje kan zaben 2027

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya ce Arewa ba za ta yi takarar shugaban kasa ba sai bayan Tinubu ya kammala wa’adinsa na biyu a 2031.

A ranar Talata ne Ganduje ya bayyana hakan yayin da ya karɓi wata tawaga daga Tinubu Media Centre da Tinubu Northern Youth Forum a hedkwatar jam’iyyar APC da ke Abuja.

Maganar Ganduje ta jawo ce-ce-ku-ce inda manyan 'yan siyasar Arewa suka masa martani a wurare daban daban.

Kara karanta wannan

An fara juyawa Tinubu, Atiku da Peter Obi baya game da zaben shugaban ƙasa na 2027

Martanin ACF ga Abdullahi Ganduje

Kungiyar ACF ta nesanta kanta daga kalaman Abdullahi Ganduje, tana mai cewa Arewa ba za ta jira har zuwa 2031 kafin ta nemi shugabancin kasa ba.

Mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya ce Ganduje bai da hurumin magana da yawun daukacin Arewa, domin ‘yan Najeriya ne ke da ikon yanke hukunci a zabe.

Wanene zai yanke hukunci a zaben 2027?

Farfesa Muhammad-Baba ya ce kalaman Abdullahi Ganduje ra’ayi ne kawai, amma masu jefa kuri’a ne za su yanke hukunci a 2027.

Ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun fahimci yadda aka ba su alkawuran da ba a cika ba a baya, don haka abin da zai ba Tinubu nasara shi ne ayyukan da ya yi, ba wai matsayinsa na dan Kudu ba.

Yayin da aka fara shirye shiryen zaben 2027, 'yan siyasa daga jam'iyyun adawa suna fatan ganin sun kwace mulki daga hannun Bola Tinubu yayin da APC ke kokarin samun nasara.

Kara karanta wannan

'Komai ya wuce': El Rufai ya fadi manyan dalilai 3 na tallata Tinubu a zaben 2023

Zaben Edo: Shaidan APC ya goyi bayan PDP

A wani rahoton, kun ji cewa shaidan da jam'iyyar APC ta gabatar a kotun sauraron shari'ar zaben gwamnan jihar Edo ya goyi bayan matsayar 'yan adawa.

Shaidar ya tabbatar da cewa an samu kuskure a zaben da ya gudana duk da cewa jam'iyyarsa ce ta samu nasara a zaben wanda hakan ya dauki hankalin 'yan kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng