Alamu Sun Kara Karfi, Gwamna na Shirin Neman Takarar Shugaban Ƙasa a 2027
- Alamu sun kara karfi kan shirin Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi na fitowa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027
- Awanni 24 da ganawar Atiku da Obasanjo, magoya bayan gwamnan Bauchi sun ƙara kaimi wajen tallata shi ga ƴan Najeriya
- Kwamishinan albarkatun kasa na Bauchi ya bayyana cewa Bala ya cancanci ya karɓi mulkin Najeriya duba da yadda yake jawo matasa a jiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Sa'o'i 24 bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, alamu sun fara nuna Gwamna Bala Mohammed na Bauchi zai nemi takara a 2027.
Magoya bayan gwamnan Bauchi sun ƙara himma wajen tallata shi domin ya fito takarar shugabancin ƙasa a babban zaɓen 2027.

Asali: Twitter
Atiku ya ja zuga zuwa gidan Obasanjo
Duk da cewa Atiku ya bayyana cewa ziyarar tasa ba ta da alaƙa da zaɓen 2027, majiyoyi sun shaidawa Leadership cewa akwai batun haɗaka da wasu 'yan adawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin waɗanda suka raka Atiku akwai tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Liyel Imoke; Sanata Abdul Ahmed Ningi; da tsohon gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal.
Bayan zaɓen 2023, Atiku ya fara ƙoƙarin haɗa jam’iyyun adawa domin tunkarar zaɓen 2027, yana aiki tare da mutanen da suka haɗa da tsohon dan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai; da tsohon minista, Chibuike Amaechi na cikin waɗanda ake ganin za su iya haɗewa da Atiku.
Gwamna na hangen kujerar shugaban kasa
A gefe guda, alamun cewa Gwamna Bala Mohammed na da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa sun fara bayyana lokacin da ya ce ba zai tsaya takara ba idan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya tsaya.

Kara karanta wannan
"Najeriya ta yi Rashi," Tinubu ya kaɗu da Allah ya yi wa fitaccen malamin Musulunci rasuwa
Atiku da Bala, dukkansu ‘yan Arewa maso Gabas ne, amma har yanzu ba a san ko jam’iyyar PDP za ta sake buɗe tikitinta ga kowane yanki ba kamar yadda aka yi a 2023.
Alamun Gwamna Bala na da shirin neman kujera lamba ɗaya ya ƙara ƙarfi a jiya, lokacin da kwamishinan albarkatun ƙasa na Bauchi, Hon. Muhammad Maiwada Bello, ya yi hira da manema labarai.
Magoya bayan Gwamna Bala sun yunkuro
Kwamishinan ya ce salon mulkin gwamnan na bai wa matasa dama ya sa ya cancanta da shugabancin Najeriya.
Muhammad Maiwada Bello ya ce Bala Mohammed ya fi sauran gwamnoni da suka gabata a jihar da faɗin ƙasar nan wajen bai wa matasa mukamai.
“Gwamnan ya kafa tarihi wajen bai wa matasa damar riƙe muƙamai masu muhimmanci fiye da kowane gwamna a Najeriya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan Bala Mohammed ya zama shugaban ƙasa, Najeriya za ta ɗaukaka da ƙarfin matasa ta fannin haɓaka kirkire-kirkire, haɗin kai, da ci gaban ƙasa.
Kwamishinan ya yi kira ga matasa da su mara wa Bala baya domin ci gaba da manufofin da ke basu dama su taka rawar gani a gina makomar ƙasa.
Atiku ya ziyarci Sanata Binani
A wani labarin, kun ji cewa ziyarar da Atiku Abubakar ya kai wa Sanata Aishatu Binani har gida ta haifar da ce-ce-ku-ce a siyasar Najeriya.
Mutane sun fara surutu kan maƙasudin wannan ziyara wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ce ta zumunci ce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng