Abinci Ya Ƙare: Gwamna Ya Tattara Duka Masu Muƙaman Siyasa, Ya Kore Su daga Aiƙi
- Gwamna Abdullahi Sule ya sallami dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa a jihar Nasarawa, ya na mai yi masu fatan alheri
- Sule, wanda bai jima da korar kwamishinoni ba ya faɗi haka ne a taron bankwana da ya yi da waɗanda lamarin ya shafa a faɗar gwamnati
- Bugu da ƙari, gwamnan ya rantsar da sabon sakataren gwamnati, Labaran Magaji, wanda shi ne tsohon kwamishinan shari'a kuma Antoni Janar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da sallamar dukkanin masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa.
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 7 ga Fabrairu, 2025 a gidan gwamnatin jihar Nasarawa da ke birnin Lafiya.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta tattaro cewa Gwamna Sule ya sallami masu rike da muƙaman siyasa ne makonni ƙalilan bayan ya rushe majalisar zartarwa ta jihar.

Kara karanta wannan
Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara
Gwamnan Nasarawa ya yi bankwana da hadimansa
Sule ya sanar da matakin a taron ban kwana da ya gudanar da manyan mashawarta, hadimai na musamman, da sauran masu rike da mukaman siyasa a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnatinsa.
A yayin jawabinsa, gwamnan ya gode masu dukka bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar a lokacin da suke rike da mukamansu.
Ya kuma bada tabbacin cewa wasu daga cikinsu na iya samun damar sake dawowa cikin gwamnati a wasu muƙaman da zai naɗa nan gaba.
Gwamna Sule ya yi sababbin nade-nade
Bayan sallamar masu riƙe da muƙaman siyasa, gwamnan ya rantsar da sabon sakataren Gwamnati, Barista Labaran Magaji, rahoton Vanguard.
Barista Labaran shi ne tsohon kwamishinan shari'a kuma Antoni-Janar na jihar wanda ya rasa muƙaminsa lokacin da gwamnan ya sallami dukkan kwamishinoni.
Baya ga haka, Abdullahi Sule ya rantsar da sabon shugaban yankin Udage da ke ƙaramar hukumar Nasarawa da shugaba da ƴan majalisar gudanarwa na kwalejin ilimi ta Akwanga.
Gwamna Sule. ya buƙaci waɗanda aka rantsar da su zage dantse kuma su taimakawa gwamnatinsa wajen cika manufofinta na alheri ga al'umma.
Ina aka kwana kan naɗa kwamishinoni?
Gwamna Sule, wanda a farkon watan Janairu ya rushe majalisar zartarwa ta jihar, ya ce tuni ya mika sunayen mutum 16 da ya zaba domin naɗa su a kwamishinoni ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.
Ana sa ran sababbin nade-nade za su kara habaka tafiyar gwamnatin Abdullahi Sule da samar da ci gaba ga al’ummar jihar Nasarawa.
APC ba ta tsoron haɗewar ƴan adawa
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule ya ce jam'iyyar APC ba ta tsoron shirin da wasu manyan ƴan adawa ke yi domin haɗe wa guri ɗaya a zaɓen 2027.
Gwamna Sule.ya ce ba ya jin tsoron haɗakar ƴan adawa domin nasarar APC ta ta'allaka ne da irin ayyukan alherin da ta kawo wa ƴan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
