Kwankwasiyya: Tsagin NNPP Ya Yi Watsi da Zaben Sabon Shugaban Jam'iyya
- Tsagin Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya yi watsi da sabon taron jam'iyya da ya gudana a ranar Talata
- A wannan babban taro ne, tashin Major na NNPP ya fitar da sabon shugaban jam'iyyar na kaa da mukarrabansa
- Tsagin Kwankwasiyya, ta bakin sakataren yada labarai, Ladipo Johnson, ya zargi tsagin Major da cewa dan aiken APC ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsagin Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, ya yi watsi da babban taron da aka gudanar a ranar Talata, inda aka zabi Dr. Agbo Major a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar na Kasa.
Wannan tsagi, wanda Kwankwaso ke jagoranta, ya jaddada cewa taron ba bisa ka’ida aka yi shi ba, kuma Dr. Ajuji Ahmed ne kadai sahihin Shugaban Jam’iyyar da aka amince da shi.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a yayin taron da tsagin Major ya gudanar, an zabi wasu manyan jami’ai na jam’iyyar da suka hada da; Oginni Olaposi a matsayin Sakataren Jam’iyya na Kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai Felix Chukwurah a matsayin mataimakin shugaban Shugaban jam’iyya (Kudu), Adetoyese Omokanye a matsayin Ma’aji, Babayo Muhammed, Mataimakin shugaban Jam’iyya (Arewa), Abdulrasaq Abdulsallam a matsayin sakataren yada labarai.
NNPP Kwankwasiyya ta yi watsi da sabon zabe
Sai dai tsagin Kwankwaso, ta bakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya bayyana cewa tsagin Major ‘yan tawaye ne.
Johnson ya jaddada cewa Dr. Ajuji Ahmed ne kawai Shugaban Jam’iyyar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) da kuma hukumomin tsaro suka amince da shi.
Ya zargi tsagin Major da kokarin yaudarar jama’a da wata takaddama maras tushe, domin a cewarsa, ba su da hurumin gudanar da sabon zaben shugabancin jam’iyyar.
Ladipo Johnson ya ce:
"Su ba mambobin jam’iyyar ba ne, kuma an kore su daga NNPP. Sun ci gaba da yin abin da ya saba wa hukuncin kotu.

Kara karanta wannan
Rikicin jam'iyyar Kwankwaso ya ƙara ɗaukar zafi, sabon shugaban NNPP na ƙasa ya bayyana
"Akwai hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja da ya hana su yin wani yunkuri na jagorancin jam’iyyar. A yanzu suna aiki ne da jam’iyyun adawa, musamman APC."
Kwankwasiyya ta barranta kanta da tsagin NNPP
Johnson ya zargi tsagin Major da yin hadaka da jam’iyyar APC a wasu batutuwa, musamman a hukuncin Kotun Koli kan zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda shi ne gwamnan NNPP daya tilo a Najeriya.
Ya kuma soki ingancin zaben Major, yana mai cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar tare da Kwankwaso ba su halarci taron ba, wanda hakan ke nuna rashin sahihancin zaben.
Johnson ya kara da cewa alamomin jam’iyyar NNPP na gaskiya sun hada da littafi da hular kammala karatu mai launin ja, tare da zargin tsagin Major da kokarin yaudarar jama’a.
Tsagin NNPP ya fitar da sabon shugaba
A wani labarin, kun ji cewa tsagin da ke adawa da jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a NNPP ya gudanar da babban taro a ranar Talata, inda aka gudanar da zabe.
An zabi Agbo Major a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na kasa, Oginni Olaposi a matsayin Sakataren jam'iyya da kuma mataimakan shugaban jam'iyya a Kudu da Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng