Rikicin Jam'iyyar Kwankwaso Ya Kara Dauƙar Zafi, Sabon Shugaban NNPP na Ƙasa Ya Bayyana

Rikicin Jam'iyyar Kwankwaso Ya Kara Dauƙar Zafi, Sabon Shugaban NNPP na Ƙasa Ya Bayyana

  • Dr. Agbo Major ya zama cikakken shugaban NNPP na tsagin da ke adawa da madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso
  • Jam'iyyar NNPP ta zaɓi sababbin shugabanninta ne a wani taro da ta gudanar ranar Talata da daddare wanda ya kai wayewar garin yau Laraba
  • A jawabinsa a wurin taron 'yan tawaren bayan rantsar da shi, Major ya ce zai jagoranci farfaɗo da NNPP domin tunkarar zaɓen 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Dr. Agbo Major ya zama sabon shugaban tsagin jam’iyyar NNPP bayan kammala babban taron jam’iyyar da aka gudanar a ranar Talata.

Taron 'yan tawayen da suka bijirewa jagorori dai ya samu halartar deleget da shugabanni na jam’iyyar NNPP daga matakin jihohi da na kasa.

Agbo Major.
Dr. Agbo Major ya zama sabon shugaban tsagin NNPP mai fada da su Kwankwaso Hoto: Dr. Agbo Major
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Vanguard ta tattaro, bayan shugaban jam'iyya na ƙasa, jiga-jigan NNPP sun zaɓi sauran ƴan kwamitin gudanarwa na ƙasa watau NWC.

Kara karanta wannan

"Ba wanda ya fi karfin doka": Gwamnan CBN da wasu kusoshin Gwamnatin Tinubu sun shiga matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sababbin shugabannin NNPP sun bayyana

Sauran waɗanda aka zaɓa a matsayin ƴan kwamitin NWC na NNPP ta ƙasa karkashin Agbo Major sun haɗa da:

1. Mr. Oginni Olaposi – Sakataren NNPP na ƙasa

2. Cif Felix Chukwurah – Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP mai kula da kudancin Najeriya.

3. Alhaji Babayo Muhammed – Mataimakin shugaban jam’iyya mai kula da Arewacin Najeriya.

4. Mista Adetoyese Omokanye – Ma’ajin NNPP na kasa

5. Abdulrasaq Abdulsallam – Sakataren yada labarai na ƙasa

6. Hajia Aisha Kade – Shugabar matan NNPP ta ƙasa

7. Cif Edward Ofomona – Shugaban matasa na ƙasa.

8. Omolara Johnson – Sakataren tsare-tsare na ƙasa

Taron ya gudana daga karfe 9:00 na dare zuwa karfe 4:00 na asuba a ranar Laraba, 5 ga watan Fabrairu, 2025.

Dalilin da ya sa tsagin NNPP ya naɗa shugabanni

A ranar 1 ga Nuwamba, 2024, wata kotu a jihar Abia ta bayar da umurnin sake tsara jam'iyyar NNPP tun daga matakin gunduma har zuwa ƙasa.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun nunawa Kwankwaso yatsa kan batun komawa jam'iyyar

Kotu ta umarci Majalisar amintattu (BoT) ta NNPP karkashin Dr. Boniface Aniebonam da ta shirya tarukan zaɓen shugabanni a kowane mataki.

Aniebonam ya bayyana cewa bisa ga hukuncin kotu, NNPP ta sanar da hukumar INEC da hukumomin tsaro matakan da ta dauka don sake gina jam’iyyar.

Sabon shugaban NNPP ya buƙaci haɗin kai

Da yake jawabi bayan rantsar da shi, sabon shugaban tsagin NNPP, Dr. Agbo Major, ya bukaci ‘yan jam’iyyar da ke fushi su dawo a haɗa kai wajen sake gina ta.

Idan za ku iya tunawa tsagin Agbo Major na faɗa da tsagin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ta kai ga sanar ɗa korarsa daga jam"iyyar.

A rahoton The Nation, Agbo Major ya ce:

“Ina godiya ga dukkan deleget da suka zaɓe ni. Ba zan yi sakaci da wannan amanar ba. A ƙarƙashina NWC zai sake gina NNPP domin fuskantar zaben 2027.”

Kara karanta wannan

Ana hasashen hadaka, jam'iyyar Kwankwaso ta yi rashi, shugaban NNPP ya koma APC

Ya kuma yi gargadi cewa za a dauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa shugabannin jam’iyyar suna aiki bisa ka’ida da manufofi da aka shimfida.

Shugaban NNPP a Gombe ya koma APC

Kuna da labarin cewa NNPP ta rasa daya daga cikin ƙusoshinta da shugaban jam'iyyar na jihar Gombe ya tattara ya koma APC mai mulki.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya karɓi tsohon shugaban NNPP, Hon. Rambi Ayala, tsohon 'dan Majalisar dokokin jihar Gombe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262