'Akwai Fa'ida Sasantawa da Tinubu': Dan Majalisar PDP Ya Shawarci Tsohon Gwamna a APC
- Dan majalisar PDP a Osun, Oluwole Oke, ya ce tsohon gwamna Rauf Aregbesola har yanzu yana da tasiri a siyasar jihar
- Dan majalisar tarayyar ya ce lokaci ya yi da ya kamata Aregbesola ya sasanta da Shugaba Bola Tinubu
- Oke ya bukaci PDP da ta yi gaggawar jawo Aregbesola zuwa jam’iyyar, yana mai cewa yana da babban tasiri kuma ba a kamata a bar shi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Osogbo, Osun - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Obokun/Oriade, Oluwole Oke, ya shawarci tsohon gwamna, Rauf Aregbesola.
Oke ya ce tsohon gwamna Aregbesola har yanzu yana da matsayi a siyasar Osun inda ya bukaci ya sasanta da Bola Tinubu.

Asali: Twitter
An shawarci tsohon gwamna ya sasanta da Tinubu
Oke, wanda aka zabe shi a karkashin jam’iyyar PDP, ya ce da shi ne Aregbesola, da ya yi sulhu da Shugaba Bola Tinubu, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan ficewar wata kungiya mai goyon bayan Aregbesola, Omoluabi Progressives daga jam’iyyar APC a Osun.
Ficensu ya biyo bayan dogon rikicin da bai sami mafita ba tsakaninsu da APC, wanda ya samo asali daga sabanin da ke tsakanin tsohon gwamna Adegboyega Oyetola da Rauf Aregbesola.
Amma wasu majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun ce rikicin da ya sa Aregbesola ya bar APC ya samo asali ne daga sabaninsa da Tinubu.
Da yake tsokaci kan lamarin siyasar Osun a shafinsa mai suna MP Oluwole Oke-BOO, dan majalisar ya ce da shi ne dan APC, da ya tabbatar da sulhu tsakanin Aregbesola da Oyetola.
Yayin da yake kira ga PDP da ta yi gaggawa wajen cin moriyar rikicin APC, Oke ya ce jam’iyyarsa ta hanzarta jawo Aregbesola, cewar The Guardian.
A cikin sakon da ya wallafa, ya ce:
"Egbon Rauf ‘Soji Aregbesola, tsohon Gwamnan Osun kuma Ministan Harkokin Cikin Gida, mutum ne mai tasiri, mai jan hankalin jama’a, kuma dan gwagwarmaya.”

Kara karanta wannan
El-Rufai ya fadi abin da zai yi idan da yana cikin gwamnatin Tinubu, ya soki yan siyasa
"Yana da matsayi kuma yana da daraja a siyasar Osun, gaskiya ne, inda ni shi ne, da na je na roƙa, na rusuna, na yi sulhu da shugabana, Tinubu.”
“Idan da ni ne dan APC a Osun, da na tabbatar na sasanta Asiwaju Gboyega Oyetola da Ogbeni."
NNPP ta roki Aregbesola ya dawo cikinta
A wani labarin, jam'iyyar NNPP a jihar Osun ta bayyana shirinta na karɓar tsohon gwamna Rauf Aregbesola da magoya bayansa, yayin da zaɓen gwamna na 2026 ke gabatowa.
Aregbesola da ƙungiyar Omoluabi Progressives sun fice daga APC saboda wariya, dakatarwa da ƙorafi ba tare da adalci ba, da cin mutuncin tsarinsu.
Shugaban NNPP a Osun, Tosin Odeyemi, ya bukaci Aregbesola ya shiga jam’iyyar, yana mai cewa hakan zai taimaka mata a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng