'Mu Hadu a 2027': Tinubu ga Yan Adawa kan Kwace Mulkinsa, Ya Fadi Abin da Ke Gabansa
- Fadar shugaban kasa ta yi watsi da shirin da wasu ‘yan adawa suke yi, tana mai cewa Shugaba Tinubu bai damu ba kuma ko a jikinsa
- Hadimin shugaban, Sunday Dare ya bayyana taron a matsayin shiri na cin mutunci da fitar da kalamai masu tayar da zaune tsaye, yana mai cewa Tinubu na kan aikinsa
- Dare ya jaddada cewa shugaba Tinubu zai mayar da hankali ne kan ci gaban Najeriya, ba takaddamar siyasa ba, kuma 'yan takara su jira zaben 2027
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi watsi da taron wasu ‘yan adawa da kuma masu suka daga cikin jam’iyyar APC.
Fadar ta watsi da duk wani shiri da suke yi inda ta ce Shugaba Bola Tinubu bai damu ba ko a gelensa.

Kara karanta wannan
Me ya yi zafi?: Atiku ya ki halartar taron manyan kusoshin PDP da aka yi a Bauchi

Asali: Facebook
Fadar shugaban kasa ta soki yan adawa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban, Sunday Dare ya wallafa a shafin X a ranar Lahadi 2 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunday Dare ya ce taron ya hada da tsofaffin abokan Tinubu a jam'iyyar APC da ke sukar shugabancinsa.
“Yayin da Shugaba Bola Tinubu ke birnin Dar es Salaam, abokan hamayya da tsofaffin abokansa sun nuna halinsu na siyasa.
“Ina tsammani, ba wani sabon abu da ya fito daga wannan taron illa shirin da muke ji kullum da yin kalamai masu tsauri.
“Girgije yana fara raguwa, lokaci zai zo, Amma yanzu, Shugaba Tinubu ba zai damu ba, Gwabzawa tana nan gaba, ba yanzu ba."
- Sunday Dare
'Abin da ke gaban Tinubu' - Fadar shugaban kasa
Dare ya taron ya hada da manyan ‘yan adawa da wasu jiga-jigan APC da ke adawa da Tinubu, Dare ya bayyana shi a matsayin mai cike da tsurku.

Kara karanta wannan
A karshe, an samu labarin rashin lafiyar da Tinubu ke fama da ita kafin zama shugaban ƙasa
Dare ya ce duk da wannan suka, Shugaba Tinubu zai ci gaba da mayar da hankali kan mulki, ba abin da zai karkatar da shi ba.
A cewarsa, Tinubu yana mai da hankali ne kan magance matsalolin tattalin arzikin Najeriya da inganta rayuwar ‘yan kasa.
“Magana daya ce, yadda za a kyautata rayuwar ‘yan Najeriya da tattaunawa mai amfani kan tattalin arziki mai dorewa.
“Wannan shekara 2025 ce, ba 2027 ba, Wadanda ke son gwada farin jininsu su jira zabe. Tinubu na kan shugabanci mai ma’ana."
- Cewar Sunday Dare
Hadimin Tinubu ya shawarci yan adawa
Dare ya shawarci masu burin tsayawa takara su jira zaben 2027, yana mai cewa Tinubu na mayar da hankali kan shugabanci ba kamfen ba.
An samu karin tashe-tashen hankula a siyasar Najeriya yayin da wasu jiga-jigan APC da ‘yan adawa ke sukar shugabancin Tinubu.
An soki matashi kan goyon bayan Tinubu
Kun ji cewa wani matashi daga jihar Sokoto ya shirya kaɗa ƙuri'arsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
Matashin mai suna Habibu Bello Mayana ya nuna cewa a shirye yake ya zaɓi shugaban ƙasan na Najeriya idan ya sake tsayawa takara.
Asali: Legit.ng