Ana Hasashen Hadaka, Jam’iyyar Kwankwaso Ta Yi Rashi, Shugaban NNPP Ya Koma APC
- Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya karbi tsohon shugaban jma'iyyar NNPP a Gombe zuwa APC
- Inuwa Yahaya ya ce duk ‘ya’yan jam’iyyar APC na da haƙƙi iri ɗaya ba tare da la’akari da tsawon zamansu a ciki ba
- Hakan ya viyo bayan sauya shekar tsohon shugaban NNPP na Gombe, Hon. Rambi Ibrahim Ayala zuwa APC lamarin da gwamna ya ce zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi da tasiri a yankin
- Shugabanni da masu ruwa da tsaki sun nuna farin cikinsu da dawowar Ayala, suna mai tabbatar da cikakken goyon bayansu gareshi da jam’iyyar gaba ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Gombe - Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban jam'iyyar NNPP a Gombe, Hon. Rambi Ayala ya koma APC.
Hon. Ayala wanda ya taba rike mukamin dan majalisar jihar Gombe a mazabar Billiri ta Gabas ya bar jam'iyyar NNPP ce a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan
Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki

Asali: Facebook
Tsohon dan majalisa ya bar NNPP zuwa APC
Sakataren yada labaran gwamnan Gombe, Isma'illa Uba Misilli shi ya yada sanarwar ficewar Ayala a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa duk ‘ya’yan jam’iyyar APC suna daidai da kowa kuma za su samu haƙƙi da kulawa ba tare da nuna bambanci ba.
Gwamnan, wanda ya fadi haka ne bayan samun wakilci Kwamishinan Muhalli, Ruwa da Gandun Daji, Muhammad Sa’idu Fawu.
"Dawowar Hon. Rambi cikin APC ya ƙarawa jam’iyya ƙarfi da armashi a Tangale Waja, muna fatan za ka ba da gudunmawa."
Muhammad Sa’idu Fawu
Gwamna Inuwa ya fadi amfanin Rambi Ayala
Fawu ya bayyana sauya shekar Hon. Rambi a matsayin ci gaba ga demukraɗiyya, yana mai ƙarfafa masa gwiwa da ya ba da gudunmawa domin ci gaban jam’iyyar.
A madadin jam’iyyar APC ta jiha, Hon. Isiyaku Abdullahi (Jarman Akko), yace suna matuƙar farin ciki da zuwan Rambi Ayala, yana mai bayyana shi a matsayin jigo a siyasar Tangale Waja.
Shugabannin ƙananan hukumomin Ɓiliri, Kaltungo da Shongom sun nuna farin ciki da zuwan Rambi APC, suna tabbatar masa da cikakken goyon bayansu.
Shugaban jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Ɓiliri, Isiyaka Zakari, da takwaransa na gundumar Ɓiliri ta Kudu, Andrew Nayako, sun bayyana cewa APC gida ne ga Rambi.
Rambi Ayali ya fadi silar shiga APC
Hon. Barista Rambi Ibrahim Ayala ya ce:
"Mun koma APC ne don dafawa ƙoƙarin Gwamna Inuwa Yahaya na samar da ribar dimukuradiyya ga al’ummarmu a Gombe."
Hon. Rambi ya bayyana gwamnan a matsayin wanda ya zamanantar da Gombe, yana mai tabbatar da cikakken goyon baya don cigaban jihar gaba ɗaya.
Legit Hausa ta yi magana da dan APC
Wani dan jam'iyyar APC, Ibrahim Mohammed ya ce tabbas Hon. Rambi Ayala mutum ne jajartacce a bangaren siyasa da rayuwa.
"Tun lokacin da Ayala ke majalisar jiha daga karamar hukumar Billiri ya taka rawar gani wurin gudanar da shugabancinsa.
- Ibrahim Mohammed
Tsohon dan takarar gwamnan NNPP ya koma APC
Kun ji cewa tsohon dan takarar gwamna a NNPP, Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai adawa a Gombe.
Hon. Mailantarki ya koma jam'iyyar PDP ne mai adawa a jihar a ranar Asabar 9 ga watan Nuwambar 2024 da ta gabata.
Asali: Legit.ng