Gwamnoni Sun Kinkimo Hanyar Tayar da Sabuwar Rigima a Jam'iyyar PDP Ta Ƙasa

Gwamnoni Sun Kinkimo Hanyar Tayar da Sabuwar Rigima a Jam'iyyar PDP Ta Ƙasa

  • Sanata Samuel Anyanwu ya sha alwashin cewa ba zai taba yarda da duk wani yunƙuri na tsige shi daga mukamin sakataren PDP na ƙasa ba
  • Wannan dai na zuwa ne bayan gwamnonin PDP sun ayyana goyon baya ga Sunday Ude-Okoye a taron da suka yi a jihar Delta
  • Anyanwu ya rubuta wasiƙar ƙorafi ga sufetan ƴan sanda na ƙasa, ya buƙaci ya ɗauki matakin daƙile rigimar da ke shirin kunnowa a hedkwatar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Alamu na nuna za a iya samun rikici a hedkwatar jam'iyyar PDP ta ƙasa da Sanata Samuel Anyanwu ya lashi takobin sa ƙafar wando ɗaya da gwamnoni.

Anyanwu, sakataren PDP na ƙasa ya ce duk wani yunƙuri na sauke shi daga muƙaminsa gayyato sabon rikici ne a babbar jam'iyyar adawa.

Kara karanta wannan

Magana ta zo karshe: Shugaban NYSC ya fadi lokacin fara biyan N77,000

Gwamnoni da Anyanwu.
Sanata Samuel Anyanwu ya yi fatali da matakin gwamnonin PDP Hoto: @PDPGovOffolicial
Asali: Twitter

Samuel Anyanwu, ya sha alwashin kin amincewa da duk wani yunkuri na tsige shi daga mukaminsa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi rigima a taron amintattun PDP

A ranar 29 ga Janairu, an samu rikici a taron majalisar amintattun PDP kan takaddama tsakanin Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, waɗanda ke rigima kan kujerar sakataren PDP.

Rikicin ya dauki hankalin jama’a har ya kai ga doke-doke kafin jami’an tsaro su shigo don dakile tashin hankalin.

Gwamnoni sun ɗauki matsaya a rigimar sakatare

Tun daga lokacin, rikicin cikin gida na PDP ya dauki sabon salo, musamman bayan da gwamnonin jam’iyyar suka bayyana goyon bayansu ga Ude-Okoye a matsayin sahihin sakataren PDP.

Wannan matsaya ta biyo bayan hukuncin da kotun daukaka ta yanke ranar 20 ga Disamba, 2024, wanda ya tabbatar da cewa Ude-Okoye ne halastaccen sakatare.

Sai dai wannan hukunci bai yi wa Anyanwu dadi ba, inda ya aika wata takardar koke ga Sufeto Janar na ‘Yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

A takardar, Anyanwu ya bayyana goyon bayan da gwamnonin suka ba Ude-Okoye a matsayin “gayyatar rikici da raina doka.”

Matakin gwamnonin PDP zai haifar da sabon rikici

Ya ce yunkurin aiwatar da shawarar da gwamnonin suka bayar na iya jefa jam’iyyar cikin rudani da rashin bin doka.

A rahoton Leadership, Anyanwu ya ce:

"Wannan yunkuri zai iya janyo rikici da kuma saba wa doka, musamman ma ganin cewa maganar har yanzu tana gaban kotu ba a yanke hukuncin karshe ba."

Ya bukaci jami’an tsaro da su dauki matakan da suka dace don hana rikicin da ke kunno kai, tare da yin kira ga kwamitin gudanarwa na PDP ya guji daukar matakan da za su sabawa hukuncin kotu.

Ya jaddada cewa yana da hakkin shigar da kara da kuma neman adalci a kan hukuncin da ya ce an yanke a kansa ta hanyoyin da ba su dace ba.

Kara karanta wannan

Abin da shugaban BoT ya faɗa a wurin taron PDP bayan an mari babban jigo a Abuja

PDP ta fara shirin karɓe mulki a 2027

A wani labarin, kun ji cewa gwamnonin da suka hau kan mulki karkashin inuwar PDP suk sake jaddada cewa za su karbi mulki daga hannun APC a 2027.

Gwamnonin sun faɗi hakan ne jim kaɗan bayan wani taro da suka gudanar a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262