Yayin da Ake Shirin Zaben Gwamna, An Fadi Shirin APC domin Kwace Mulki cikin Sauki
- Obiora Okonkwo ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar gwamnan Anambra a 2025, yana mai alkawarin kawo shugabanci nagari da ci gaban tattalin arziki
- Farfesan ya bayyana shirin inganta tsaro, samar da ayyukan yi, da karfafawa matasa ta hanyar horas da su sana’o’i don inganta rayuwarsu da jihar gaba ɗaya
- Okonkwo ya bukaci hadin kan ‘yan Anambra domin kawo sauyi, yana mai cewa yana da cancanta fiye da tsarin rabon mukamai a siyasar jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a watan Nuwambar 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Awka, Anambra - Wani ɗan kasuwa kuma Shugaban kungiyar United Nigeria Airlines, Prof. Obiora Okonkwo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Anambra a APC.
Dan kasuwar zai nemi ya fito ne a karkashin jam'iyyar APC yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamna a ranar 8 ga Nuwambar 2025 nda zai gwabza da Gwamna Charles Soludo.

Asali: Facebook
Kusa a APC ya fadi shirinsu a zaben gwamna
Farfesa Obiora ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaɓensa, inda masoya da ‘yan jam’iyya da masu goyon baya suka taru a gidansa da ke Idemili ta Arewa, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okonkwo ya ce yana son zama gwamna ne don karɓe mulki daga Gwamna Chukwuma Soludo, domin ya mayar da Anambra jiha mai kyakkyawan shugabanci da ci gaba.
Ya ce da wannan kwamitin yakin zaɓe, an shirya tsaf domin takarar gwamna a 2025 tare da gabatar da shirinsa na inganta jihar.
Jigon APC ya fadi burinsa game da Anambra
Yayin jawabinsa, ya bayyana burinsa na samar da Anambra mai inganci, aminci, da daidaituwar tattalin arziki, yana mai cewa matsalolin tsaro da rashin ayyukan yi sun hana jihar ci gaba.
Ya bukaci sabuwar tafiya, yana roƙon mutanen Anambra su haɗu domin kawo sauyin tattalin arziki, tsaro, da shugabanci nagari, cewar Tribune.
Jigon APC ya gargadi Tinubu kan Kwankwaso
Kun ji cewa jigon APC a Kano, Musa Ilyasu Musa Kwankwaso ya gargadi shugabannin jam'iyyar da su yi taka tsan-tsan kan shirin shigowar Rabiu Kwankwaso.
Ilyasu ya zargi Sanata Kwankwaso da kokarin amfani da APC ne kawai domin tabbatar da wa’adin Gwamna Abba Kabir Yusuf a 2027, ba don amfanin jam’iyyar ba.
Kusan na APC ya bukaci Tinubu da ya yi nazari kan tarihin siyasar Kwankwaso, yana mai cewa ya saba cin amana a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng