Kusa a APC Ya Fadi Abin da Zai Faru idan Kwankwaso Ya Dawo Jam'iyya, Ya Gargadi Tinubu
- Jigon APC a Kano, Musa Ilyasu Musa Kwankwaso ya gargadi shugabannin jam'iyyar da su yi taka tsan-tsan kan shirin shigowar Sanata Rabiu Kwankwaso
- Musa Ilyasu ya zargi Kwankwaso da kokarin amfani da APC ne kawai domin tabbatar da wa’adin Abba Kabir Yusuf a 2027, ba don amfanin jam’iyyar ba
- 'Dan siyasar wanda babba ne a APC ya bukaci Tinubu da ya yi nazari kan tarihin siyasar Kwankwaso, yana mai cewa ya saba cin amana a baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - Kusa a APC, Ilyasu Musa Kwankwaso ya gargadi Shugaba Bola Tinubu da shugabannin APC da su yi taka tsan-tsan kan shirin Sanata Rabiu Kwankwaso.
Tsohon kwamishina a jihar Kano ya ce kokarin da Kwankwaso ke yi na komawa jam’iyyar makirci ne.

Kara karanta wannan
Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki

Asali: Facebook
Jigon APC ya gargadi Tinubu da APC
Da yake magana da ‘yan jarida a Kano, ya ce ko da yake Kwankwaso na da ‘yancin komawa APC, dole ne shugabannin jam’iyyar su yi taka tsan-tsan, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ilyasu Kwankwaso ya ce wannan mataki na iya haifar da rikici da rarrabuwar kai a APC, saboda ana iya samun wasu boyayyun manufofi da ba su da alfanun jam’iyyar.
Ya bayyana cewa Sanata Kwankwaso yana kokarin samun yardar Tinubu ne domin shiga APC don tabbatar da wa’adin Gwamna Abba Kabir Yusuf a 2027.
Ya yi ikirarin cewa Kwankwaso na shirin sauya sheka ne domin kaucewa matsalolin cikin gida na NNPP, don gujewa rasa tasiri a zaben 2027.
“Mun san yunkurin Kwankwaso na samun Tinubu ya amince da shigarsa APC don Gwamnansa ya samu wa’adi na biyu ba tare da matsala ba.”
"Tinubu ya tambayi Atiku, Jonathan da wasu da suka taba shan kaye a hannun Kwankwaso.”
- Musa Ilyasu Kwankwaso
'Yadda Kwankwaso ke yaudara' - Ilyasu Kwankwaso
Ilyasu Kwankwaso ce tarihi ya nuna cewa Kwankwaso ya taba yin hadaka da Atiku, amma daga baya ya juya masa baya kamar yadda ya yi wa Jonathan a 2015.
Bayan haka, ya ce Kwankwaso ya fice daga APC zuwa PDP, sannan daga PDP zuwa NNPP, yana ci gaba da barin jam’iyyu bayan amfani da su.
Hon. Kwankwaso ya yi hasashen cewa matakin da Kwankwaso ya dauka kan Ganduje a 2015 na iya sake faruwa da Tinubu a 2027 idan aka karɓe shi cikin APC.
Tinubu ya ba Ilyasu Kwankwaso mukami
Kun ji cewa Hon. Musa Ilyasu Kwankwaso ya samu muƙami a gwamnatin Bola Tinubu a yau Laraba 18 ga watan Disambar 2024.
Tinubu ya amince da nadin Ilyasu Kwankwaso da Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi a hukumar raya kogunan Hadejia-Jama’are.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng