Gwamnonin PDP Sun Dauki Matakin Kayar da Bola Tinubu a 2027

Gwamnonin PDP Sun Dauki Matakin Kayar da Bola Tinubu a 2027

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun ce za su karbi mulki daga hannun APC a zaben shugaban kasar Najeriya da za a gudanar a shekarar 2027
  • Bayan wani taro da suka gudanar a jihar Delta, gwamnonin sun yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu da ta sauya manufofin tattalin arzikinta
  • Haka zalika gwamnonin sun tabbatar da shirin warware rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar da suke fama da su tun bayan zaben 2023

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Gwamnonin PDP sun bayyana tabbacin cewa jam’iyyarsu za ta kayar da APC a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Gwamnonin sun bayyana hakan ne bayan wani taro da suka gudanar a Asaba, babban birnin jihar Delta, inda suka fitar da sanarwa mai dauke da abubuwa guda bakwai.

Kara karanta wannan

Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki

Gwamnonin PDP
Gwamnonin PDP sun sha alwashin kifar da Tinubu a 2027. Hoto: Lawal Muazu Bauchi
Asali: Twitter

Hadimin gwamna Bala Mohammed, Lawal Muazu Bauchi ya wallafa a Facebook cewa gwamnonin sun yi kira ga Bola Tinubu kan tsare tsaren tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta wallafa cewa taron ya gudana ne bayan wani sabani da aka samu a taron PDP a Abuja inda aka ba hamata iska.

Shirye-shiryen PDP na karbar mulki a 2027

Gwamnonin PDP sun bayyana cewa suna da yakinin jam’iyyar za ta dawo kan karagar mulki a matakin tarayya a shekarar 2027.

A cewar gwamna Bala Mohammed:

“Mun yarda cewa PDP ce ke da mafita ga matsalolin Najeriya,
"Kuma muna da tabbacin cewa ‘yan Najeriya za su dawo gare mu domin sake farfado da arzikin da kasar nan ta yi kafin 2015.”

Gwamnonin sun kuma jaddada cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga kauye cikin dare sun yi wa mutane yankan rago

Haka zalika sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da nuna juriya duk da kalubalen da ake fuskanta a kasar.

Kiran PDP ga Tinubu kan tattali

A cikin sanarwar bayan taron, gwamnonin PDP sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba manufofin tattalin arzikin gwamnatinsa.

Sun ce halin kuncin da ‘yan Najeriya ke ciki na bukatar gaggawar sauya tsare-tsare domin rage radadin da jama’a ke sha.

Sanarwar ta ce:

“Mun yaba wa gwamnonin PDP kan yadda suka dauki matakan rage wahalar da jama’arsu ke ciki, tare da gina tubalin ci gaba mai dorewa a jihohinsu,”

Warware rikicin jam’iyyar PDP

Gwamnonin PDP sun bayyana gamsuwarsu da yadda kwamitin gudanarwar jam’iyyar na kasa (NWC) ke kokarin shawo kan matsalolin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta.

Sun yi kira da a ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna, musamman kan batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP 12 sun shiga ganawar sirri yayin da rikicinta ke neman ɗaiɗaita ta

Haka zalika, gwamnonin sun nuna goyon bayansu ga hukuncin kotun daukaka kara da ya shafi rikicin shugabancin jam’iyyar, tare da bukatar NWC da ta aiwatar da hukuncin yadda ya kamata.

Shirye-shiryen taron NEC na PDP

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa an kammala duk wasu sharuda na doka da suka dace domin gudanar da sahihin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar.

“Wannan taro na farko a sabuwar shekara ya ba mu damar duba halin da kasa ke ciki, da kuma nazarin yadda PDP ke gudanar da mulki a jihotanta,
"Musamman a bangarorin gine-gine, tattalin arziki da tsaro,”

- Bala Mohammed

NEF ta bukaci Tinubu ya saki Farfesa Yusuf

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar dattawan Arewa sun kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kama tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf.

Kungiyar dattawan Arewa ta NEF ta ce bai kamata a rika kama wanda suke caccakar gwamnati ba da sunan yaki da cin hanci da rashawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel