‘Ku Manta da 2027’: Jam’iyyar Adawa ga PDP, Ta Nemo Hanyar Kwace Mulkin Tinubu

‘Ku Manta da 2027’: Jam’iyyar Adawa ga PDP, Ta Nemo Hanyar Kwace Mulkin Tinubu

  • Jam’iyyar LP ta bukaci PDP ta manta da shiga zaben 2027, tana mai cewa jam’iyyar ta rasa shugabanci da alkibla.
  • Jam'iyyar ta ce PDP ta gagara shiryawa tun bayan rasa mulki a 2015, don haka ba za ta iya kwace mulki a 2027 ba
  • LP mai adawa ta bukaci PDP da ta hada kai da ita domin su yi aiki tare wajen kwace mulki daga APC a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Abeokuta, Ogun - Jam’iyyar LP ta shawarci jam’iyyar da ta manta da shiga zaben 2027, tana mai cewa ta rasa shugabanci da alkibla.

LP ta ce rikicin shugabanci da ke addabar PDP da zargin da dan takararta na 2023, Alhaji Atiku Abubakar na ba ‘yan adawa N50m don su gurgunta dimukuradiyya ya nuna cewa PDP ba ta da karfin jagoranci.

Kara karanta wannan

Bayan ba hammata iska a taron PDP, Sanata ya gaji da lamarinta, ya tuba zuwa APC

Jam'iyyar LP ta shawarci PDP kan kwace mulkin Tinubu a 2027
Jam'iyyar ta soki matsalolin PDP inda ta nemi su hada kai domin kawace mulkin Tinubu a zaben 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi.
Asali: Facebook

LP ta shawarci jam'iyyar PDP kan zaben 2027

Sakataren yada labaran LP na kasa, Abayomi Arabambi shi ya bayyana haka a Abeokuta da ke jihar Ogun, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arabambi ya ce PDP ta kasa shiryawa tun bayan da ta rasa mulki a hannun APC a 2015, don haka zai yi wahala ta sake kwace mulki a 2027.

Ya ce, idan har PDP za ta dauki shawara, ya kamata ta janye daga takarar 2027 ta hada kai da LP domin su zama karfi guda wajen kwace mulki daga APC.

“Domin gujewa irin abin da ya faru a 2023, dole PDP da LP su hada kai su tsaya a matsayin jam’iyya daya don kada su sake raba kuri’unsu.
“PDP tana cikin rikicin shugabanci mai tsanani, idan ba ta iya daidaita kanta ba, ta yaya za ta iya tafiyar da harkokin kasa?”

- Abayomi Arabambi

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun raba gari da gwamnatin Tinubu kan kama Farfesa Yusuf

LP ta musanta zargin Atiku kan yan adawa

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da zargin Atiku, yana mai cewa APC da shugaba Tinubu ba su da alhakin rikicin da ke cikin PDP, don kuwa rikicin nasu ne suka haddasa.

Arabambi ya ce jam'iyyar LP ta samu fiye da kuri’u miliyan shida a 2023, don haka idan PDP ta hada kai da ita, tabbas za su samu nasara a 2027, The Nation ta ruwaito.

Ya ce ba sa son abin da ya faru a 2023 ya sake faruwa, inda PDP da LP suka raba kuri’unsu, don haka ya zama dole su hada kai domin kayar da APC a 2027.

Sanatan PDP ya yi watsi da ita

A baya, kun ji cewa bayan jita-jita na watanni da dama, Ned Nwoko ya fice daga jam’iyyar PDP kuma ya koma APC, yana mai bayyana rikice-rikicen jam’iyyar a matsayin dalilai.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

Sanata Nwoko ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta rabu gida biyu, inda rikicin cikin gida ya hana ci gaba, lamarin da ya sa dole ya sauya sheka.

A cikin wasikar murabus dinsa, Nwoko ya ce yana fatan ci gaba da aiki don amfanin jama’a, duk da cewa ya bar PDP mai adawa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel