"Kwankwaso na Shirin Ficewa daga NNPP zuwa APC," An Faɗi Abin da Ya Hango a 2027

"Kwankwaso na Shirin Ficewa daga NNPP zuwa APC," An Faɗi Abin da Ya Hango a 2027

  • Musa Iliyasu Kwankwaso ya zargi madugun Kwankwasiyya da shirin shiga jikin Bola Tinubu saboda ya cimma wani burinsa na siyasa
  • Tsohon kwamishinan kuma jigon APC ya tunatar da Tinubu irin cin amanar da Kwankwaso ya yi wa Atiku Abubakar da Goodluck Jonathan a baya
  • Sai dai shugaban NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa ya ce wannan duk shaci faɗi ne, babu wanda zai koma jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Tsohon kwamishina a Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso na shirye-shiryen sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Musa Iliyasu ya bayyana cewa Kwankwaso na ƙoƙarin shiga jikin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu saboda yana son Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi tazarce a 2027.

Musa Iliyasu da Kwankwaso.
Jigon APC a Kano ya ce Kwankwaso na shirin dawowa jam'iyya mai mulki Hoto: Musa Iliyasu Kwankwaso, Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Kwankwaso na son Tinubu ya karbe shi a APC

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ba za ta raga ba," Abba Gida Gida ya zare takobin yaki da rashawa

Jigon APC ya yi wannan ikirarin ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon kwamishina kuma daraktan kudi na Hadejia Jama’are River Basin Development Authority, ya ce Kwankwaso na son komawa APC ne don cimma burinsa na siyasa.

"Muna sane da kokarin da Kwankwaso ke yi na shiga jikin shugaba Tinubu ya samu ƙofar shigowa APC, hakan zai ba gwamnansa damar samun wa’adi na biyu ba tare da matsala ba," in ji shi.

Musa Iliyasu ya gargaɗi Bola Tinubu

Ya gargadi Tinubu da kada ya amince da Kwankwaso, yana mai tunatar da shi yadda tsohon gwamnan Kano ya taba cin amanar Atiku Abubakar da Goodluck Jonathan a baya.

"Tinubu ya tambayi Atiku da Jonathan abin da Kwankwaso ya yi masu. Ya taba marawa Atiku baya, amma daga baya ya bar shi.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

"A lokacin Jonathan, ya nuna kamar yana tare da shi, amma daga baya ya koma APC a 2015," in ji Musa Iliyasu.

Musa Iliyasu ya yi zargin cewa bayan barin APC a 2019 zuwa PDP, Kwankwaso ya koma NNPP a 2023 ne kawai domin rage wa Atiku kuri’u a Kano.

"Bayan ya rage wa Atiku kuri’u a Kano, Kwankwaso bai iya zama a PDP ba, ya sake tsallakawa zuwa NNPP, ya ƙyale Tinubu a lokacin."
"Yawancin ‘yan majalisar wakilai da suka lashe zabe a karkashin NNPP yanzu sun haɗe da APC. Ba da dadewa ba, Kwankwaso zai zama dan siyasa maras mafaka," in ji Musa Iliyasu.

NNPP ta karyata zargin komawa APC

Sai dai shugaban NNPP a Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya musanta batun cewa manyan jiga-jigan jam’iyyar na shirin komawa APC.

"Mu da muke shugabanni da masu ruwa da tsaki a NNPP muna nan daram tare da gwamnanmu.

Kara karanta wannan

A karshe, an samu labarin rashin lafiyar da Tinubu ke fama da ita kafin zama shugaban ƙasa

"Gwamnanmu na aiki tukuru, hatta a Najeriya, babu gwamna da ya kai shi iya aiki. Me za mu samu idan muka bar NNPP zuwa APC?" in ji shi.

Hadimin Kwankwaso ya shiga gwamnatin Abba

A wani labarin kun ji cewa hadimin Rabiu Musa Kwankwaso ya samu muƙami a gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir ya nada Ibrahim Adam, tsohon hadimin Kwankwaso a matsayin mai ba gwamnatin Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262