Zaben 2027: El Rufai da Sauran Tsofaffin Gwamnonin da Za Su Iya Gwabzawa da Tinubu

Zaben 2027: El Rufai da Sauran Tsofaffin Gwamnonin da Za Su Iya Gwabzawa da Tinubu

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya taso jam’iyyar APC a gaba a cikin ƴan kwanakin nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

A ranar Litinin, 27 ga Janairu, El-Rufai ya sake sukar APC, inda ya yi zargin cewa jam’iyyar mai mulki na shirin ruguza jam’iyyun adawa kafin zaɓen 2027.

El-Rufai zai iya takara da Tinubu
Tsofaffin gwamnonin da za su iya takara da Tinubu a 2027 Hoto: @IU_Wakili, @DOlusegun, @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Tsofaffin gwamnonin da za su iya takara da Tinubu

Ana hasashen cewa Nasir El-Rufai na iya tsayawa takara da shugaba Bola Tinubu a 2027, duba da yadda yake ƙara sukar gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai, wanda ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa APC, ya yi wannan zargi ne yayin da yake jawabi a wani taro da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton TheCable.

Wasu masu nazarin siyasa na ganin sukar da tsohon gwamnan Kaduna ke yi ba ya rasa nasaba da gazawarsa wajen samun wani muƙami a gwamnatin Bola Tinubu, duk da rawar da ya taka wajen samun nasarar APC.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya fadi abin da zai yi idan da yana cikin gwamnatin Tinubu, ya soki yan siyasa

A cikin wannan rahoton, Legit hausa ta lissafo wasu tsofaffin gwamnoni uku na Najeriya da ka iya tsayawa takara da Tinubu a zaɓen 2027.

1. Nasir El-Rufai

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
El-Rufai na iya takara da Tinubu a 2027 Hoto: @IU_Wakili
Asali: Twitter

Nasir El-Rufai ya kasance gwamnan jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023. Ya taɓa zama ministan babban birnin tarayya Abuja daga 2003 zuwa 2007.

Bayan da majalisar dattawa ta ƙi amincewa ya samu muƙamin minista a 2023, El-Rufai mai shekara 64 a duniya ya ɗan nesanta kansa daga harkokin jam'iyyar APC.

A cikin ƴan kwanakin nan, El-Rufai ya halarci wani taro tare da Manjo Hamza Al-Mustapha, Shehu Musa Gabam, shugaban jam’iyyar SDP da Segun Showunmi, mai fafutukar kafa sabuwar tafiya ta siyasa.

Ana hasashen zaman nasu dai, ba ta rasa nasaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

2. Rabiu Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
Kwankwaso zai iya sake tsayawa takara a zaben 2027 Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Rabiu Kwankwaso ya yi gwamnan jihar Kano daga shekarar 1999 zuwa 2003, sannan daga 2011 zuwa 2015.

Bayan da ya yi rashin nasarar komawa mulkin Kano a 2003, an naɗa shi a matsayin ministan tsaro a jamhuriya ta huɗu, daga 2003 zuwa 2007, a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan

Gwamoni sun kira taron gaggawa bayan an ba hamata iska a taron PDP

Daga bisani, an zaɓe shi matsayin sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a shekarar 2015, inda ya yi wa’adi ɗaya a ƙarƙashin APC.

Daga baya, ya koma jam’iyyar PDP bayan dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da gwamnan Kano na wancan lokacin, Abdullahi Umar Ganduje.

A watan Maris na shekarar 2022, Kwankwaso ya fice daga PDP inda ya koma jam’iyyar NNPP, wacce yake ciki a halin yanzu.

Ana hasashen cewa Kwankwaso zai sake gwada sa'arsa wajen neman shugabancin Najeriya, bayan ya yi rashin nasara a zaɓen 2023 a hannun Shugaba Bola Tinubu.

3. Peter Obi

Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi
Peter Obi na iya sake jaraba sa'arsa a zaben 2027 Hoto: @Peterobi
Asali: Twitter

Peter Obi ya kasance gwamnan jihar Anambra daga ranar 17 ga watan Maris, 2006, zuwa ranar 3 ga watan Nuwamba, 2006, lokacin da aka tsige shi.

An mayar da shi kan mulki a ranar 9 ga Fabrairu, 2007, inda ya ci gaba da wa’adinsa har zuwa 2010.

Jaridar Vanguard ta ce Peter Obi ya sake cin zaɓe na wa’adi na biyu a shekarar 2010, wanda ya kare a ranar 7 ga Maris, 2014.

Kara karanta wannan

"Daga Amurka aka samo kudin," Dattijo ya tona yadda aka nemi hana Tinubu takara

Tun daga shekarar 2022, Obi yake a jam’iyyar LP, wacce ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashinta a zaɓen 2023.

El-Rufai ya musanta shirin barin APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa yana shirin ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ko kaɗan ba shi da wani shiri na raba gari da jam'iyyar APC wacce ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa ta.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana sukar jam'iyyar ne saboda kawai yana son ta gyara yadda take gudanar da al'amuranta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel