Me Ya Yi Zafi? Atiku Ya Ki Halartar Taron Manyan Kusoshin PDP da Aka Yi a Bauchi

Me Ya Yi Zafi? Atiku Ya Ki Halartar Taron Manyan Kusoshin PDP da Aka Yi a Bauchi

  • Atiku Abubakar bai halarci taron PDP na Arewa maso Gabas ba, bai kuma aika wakili ko bayar da hakuri kan rashin zuwansa ba
  • Shugaban riko na PDP, Umar Ilya Damagum ya bukaci kusoshin jam'iyyar da su daina rikici da junansu wanda ke kawo rarrabuwar kai
  • A wajen wannan taro, PDP ta yanke shawarar sauya shugabanci a jihohi, tare da kokarin dawo da tsoffin shugabanni cikin jam’iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, bai halarci taron PDP na shiyyar Arewa maso Gabas ba a Bauchi a ranar Alhamis.

Taron ya samu halartar gwamnonin PDP guda uku: Bala Mohammed na Bauchi, Dr. Agbu Kefas na Taraba, da Ahmad Umar Fintiri na Adamawa.

Gwamnan Bauchi ya yi magana kan shugabancin PDP a taron kusoshin jam'iyyar
Atiku Abubakar ya ki halartar taron kusoshin PDP na shiyyar Arewa maso Gabas. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Atiku bai halarci taron PDP a Bauchi ba

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

Hakanan, sanatoci, ‘yan majalisun tarayya da ‘yan majalisun dokoki na jihohin shiyyar sun halarci taron kusoshin jam’iyyar ta PDP, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa Atiku bai aika wakili ba kuma bai bayar da hakuri kan rashin halartarsa ba, sabanin sauran manyan ‘yan jam’iyyar.

An tattauna batutuwan da suka shafi shirye-shiryen babban taron jam’iyyar na shiyyar da kuma na kasa da ke tafe.

Shugaban PDP ya gargadi 'yan jam'iyya

Shugaban riko na PDP, Amb. Umar Ilya Damagun, ya bukaci shugabanni su daina rikici da juna wanda shi ke kawo rarrabuwar kai a jam’iyyar.

Damagun ya ce:

“Sha’awa da muradi suna da muhimmanci, amma babu wanda zai cimma burinsa idan jam’iyyar ba ta da karfi.”

Damagun ya ce PDP jam’iyya ce mai karfi kuma mai tarihi, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ta fi karfin ace ta mutum guda ce.

“Ba na wakiltar wani mutum. Jam’iyya ta fi kowanne mutum. Za mu ba mutum dukkanin goyon baya amma idan muka ga kana kauce hanya, sai mu rabu da kai.”

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya kara girgiza siyasar Najeriya bayan ganawa da 'yan jam'iyyar SDP a Abuja

- Umar Damagun.

Gwamna ya kawo sauye-sauye a shugabancin PDP

Gwamnan Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP ya jaddada cewa PDP na da karfi kuma gwamnoni za su goyi bayan cigabanta.

Bala Mohammed ya ce domin tabbatar da ganin an yi sulhu, za a sauya tsarin shugabanci a tsakanin jihohi, wanda zai rage rikice-rikice.

Ya ce mukaman PDP a Gombe za a mayar da su Bauchi, na Borno za a mayar da su Yobe, na Adamawa kuma za a mayar da su Taraba.

Gwamnan ya ce shugabannin PDP a shiyyar za su yi aiki tare don rage rabuwar kai da kuma dawo da tsofaffin shugabannin jam'iyyar da suka barta.

Bala Mohammed ya ce za su marawa tsohon shugaban PDP na shiyyar baya, su dawo da shi cikin jam’iyya tare da mutunta shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.