'Talauci ne': Ministan Buhari Ya Fadi Dalilin Shiga Siyasa, Ya Bugi Kirji kan Kafa APC

'Talauci ne': Ministan Buhari Ya Fadi Dalilin Shiga Siyasa, Ya Bugi Kirji kan Kafa APC

  • Tsohon Ministan Sufuri a gwamnatin tarayya, Rotimi Amaechi, ya bayyana dalilin fadawarsa cikin siyasa ba ji ba gani
  • Rt. Hon. Amaechi ya bayyana cewa talauci ne ya sa ya tsaya tsayin daka a siyasa tun bayan kammala jami'a a shekarar 1987
  • Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa ‘yan siyasa a Najeriya suna amfani da mukamansu ne don sata, cin zarafi, da kuma riƙe mulki ta kowace hanya
  • Ya ce ba za a iya shafe rawarsa a kafa jam’iyyar APC ba, kuma a dalilin tsayuwar daka, PDP da Goodluck Jonathan sun mika mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa talauci da buƙata ne suka tilasta masa kasancewa cikin siyasa tun bayan kammala jami’a a 1987.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya tona asirin yadda suka dauki hayan mata domin kifar da Jonathan

Tsohon gwamnan Rivers ya fayyace irin muhimmiyar rawar da ya taka yayin kafa jam'iyyar APC a Najeriya inda ya ce babu wanda zai raina tasirinsa a siyasa.

Amaechi ya fadi dalilin shiga siyasa
Rotimi Amaechi ya ce talauci ne ya tilasta shi shiga siyasa. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Amaechi.
Asali: Facebook

Rotimi Amaechi ya yi alfahari da kafa APC

Amaechi ya bayyana hakan ne a bidiyo da Punch ta wallafa yayin taron ƙasa kan ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya da aka gudanar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya ƙara da cewa kasancewarsa a siyasa, musamman jam’iyyar APC, ya sa ba za a iya shafe rawarsa ba cikin harkokin siyasa a Najeriya.

Ya koka da halayen yan siyasa musamman a lokutan zaɓe inda suke yaudarar mutane da kudi.

Musabbabin shigan Amaechi siyasa bayan gama jami'a

“Abin takaici, talauci ne ya sa na kasance a siyasa tun bayan barin jami’a a 1987, kuma har yanzu ina cikin tsarin.
“Ba za ku iya shafe rawar da na taka a kafa jam’iyyar APC ba, kuma ba za ku iya shafe rawata a yadda ta ci zaɓe ba, ba zai yiwu ba."

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya tona asirin APC a Jonathan

Kun ji cewa tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana yadda suka biya mata don yin zanga-zanga a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Tsohon gwamnan Rivers ya ce ya sha mamaki a lokacin da ya je wurin taron domin gane wa idonsa yadda shirin ke tafiya inda suka yaudare su.

Amaechi ya caccaki masu jefa kuri'a a Najeriya, yana cewa yawancinsu suna bin 'yan siyasa ne saboda kyauta da alkawarin kudi da suke yi a lokutan zaɓe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel