El Rufai Ya Fadi Abin da Zai Yi Idan da Yana cikin Gwamnatin Tinubu, Ya Soki Yan Siyasa

El Rufai Ya Fadi Abin da Zai Yi Idan da Yana cikin Gwamnatin Tinubu, Ya Soki Yan Siyasa

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya musanta ikirarin neman mukami a gwamnatin Bola Tinubu, yana mai cewa ya riga ya bayyana matsayinsa
  • El-Rufai ya zargi wasu masu kare gwamnatin Tinubu da fifita bukatunsu akan gaskiya, yana mai cewa biyayya ga Allah da kasa ta fi kowanne muhimmanci
  • Tsohon gwamnan ya ce ko da kuwa yana cikin gwamnatin Bola Tinubu zai caccake tsarinsa idan ya ga abin da bai dace ba kamar yadda ya ce ya yi a da
  • Wannan na zuwa ne bayan Daniel Bwala ya kalubalanci Malam El-Rufai a shafin X, yake tambata ko zai soki APC idan har yana cikin gwamnatin Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya mayar da martani kan zargin sukar APC saboda bai cikin gwamnatin.

Kara karanta wannan

'Ka rike matsayinka': El-Rufai ya yi martani ga hadimin Tinubu, ya ce bai son kujerar minista

El-Rufai wanda yana daya daga cikin jiga-jigan da suka kafa jam’iyyar APC, Nasir ya karyata rade-radin cewa yana neman mukami a gwamnati.

El-Rufai ya mayar da martani kan zargin sukar APC saboda bai cikin gwamnati
Nasir El-Rufai ya ce ko da yana cikin gwamnatin Bola Tinubu ba zai hana shi sukarta ba. Hoto: Nasir El-Rufai, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Daniel Bwala ya kalubalanci Nasir El-Rufai

El-Rufai ya fadi haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X yayin martani ga hadimin Bola Tinubu, Daniel Bwala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan kalubalantar El-Rufai da Daniel Bwala ya yi inda ya sokeshi bisa kalamansa kan APC, yana cewa jam’iyyar ta kauce daga akidunta.

A taron kasa a Abuja kan karfafa dimokuradiyya, El-Rufai ya bayyana halin da Najeriya ke ciki a matsayin “gaggawar kasa” bisa tabarbarewar mulki da adawa.

Bwala ya yi martani a shafin X, yana kalubalantar El-Rufai ko zai soki APC kamar haka idan har yana cikin gwamnatin Tinubu.

El-Rufai ya fadi matsayarsa ko da yana gwamnati

El-Rufai ya mayar da martani da cewa da yana cikin gwamnati, da har yanzu yana fadin irin wadannan kalamai, domin tun farko bai nemi mukami ba.

Kara karanta wannan

'Babu Ministan Tinubu da ya fi shi': Jigon APC ya kare El Rufai, ya hango kuskuren jam'iyya

"Da ina ci gaba da kasancewa a cikin gwamnatin Tinubu, zan faɗi ko aikata abin da na yi yanzu kan wannan bala’i da ya faru a cikin jam’iyyar da na taimaka kafa, da kuma gwamnatin da ta fito daga cikinta.
"Da farko zan yi hakan cikin zaman sirri tare da wadanda abin ya shafa, sannan in fito fili idan ba a ɗauki matakan gyara ba. Ku tafi ku duba tarihin aikina a hidimar jama’a tun daga 1998."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya kuma soki wadanda ke kare gwamnatin Tinubu komai ta yi, yana cewa sun fi damuwa da moriyarsu fiye da gaskiya, inda ya bukaci su fifita biyayya ga Allah.

El-Rufai ya yi magana kan makomarsa a APC

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya yi magana kan rahotannin da ake yaɗawa na cewa yana shirin barin jam'iyyar APC.

Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ko kaɗan ko kaɗan bai da shirin barin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya da ya yi gwamna har sau biyu a ƙarƙashinta.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan El Rufa'i ya kwance mata zani a kasuwa

Malam El-Rufai ya bayyana cewa yana matsawa jam'iyyar APC ne saboda yana so ta gyara yadda take gudanar da harkokinta a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel