A Ƙarshe, An Samu Labarin Rashin Lafiyar da Tinubu Ke Fama da Ita Kafin Zama Shugaban Ƙasa

A Ƙarshe, An Samu Labarin Rashin Lafiyar da Tinubu Ke Fama da Ita Kafin Zama Shugaban Ƙasa

  • Tsohon gwamnan Osun, Bisi Akande ya tabbatar da cewa Bola Tinubu na fama da ciwon ƙafa kafin ya zama shugaban ƙasa a 2023
  • Akande ya bayyana yadda Tinubu ya faɗa masa matsalar ƙafarsa a lokacin da yake kokarin shawo kansa ya nemi kujera lamba ɗaya
  • Ya ce a farko Tinubu ba ya son jin maganar shugabancin Najeriya kuma duk wanda ya je masa da maganar ba su karewa lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Dattijon kasa kuma tsohon gwamnan Osun, Pa Bisi Akande, ya bayyana tattaunawar da ya yi da Shugaba Bola Tinubu a lokacin da ake tunkarar zaben 2023.

Akande ya bayyana cewa Bola Tinubu ya koka kan ciwon da yake fama da shi a ƙafarsa kafin ya amince zai nemi takarar shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samo rancen sama da N1bn don tsame Najeriya daga duhu

Bisi Akande.
Bisi Akande ya ce tun kafin Tinubu ya tsaya takara, ya koka kam ciwon kafar da yake fama da shi Hoto: Chief Bisi Akande
Asali: Twitter

A wata hira da ya yi da dan jarida Edmund Obilo wacce aka wallafa a Youtube, Akande ya bayyana wasu muhimman abubuwa game da yadda Tinubu ya zama shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu bai san siyasar ƙasa ba kafin 2023

Ya ce ko da yake Tinubu ya kasance kwararren mai tsara dabarun siyasa, amma kafin ya zama shugaban kasa bai da cikakken fahimta game da siyasar Najeriya.

"Yana iya sanin abubuwa da dama game da siyasar Legas da Amurka, amma bai san komai ba kan siyasar Najeriya. Yanzu da ya zama shugaban kasa, ban sani ba ko ya koyi abubuwa da yawa," in ji Akande.

Akande ya musanta batun da ake cewa tun usuli burin Tinubu shi ne ya shugabanci kasar nan.

Dattijon ƙasar ya ce shi ne ya matsa masa lba har ya shawo kansa ya amince da tsayawa takara amma a farko duk wanda ya je masa da maganar ba su ƙarƙarewa lafiya.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna ya tono abin da ƴan Najeriya ba su sani ba game da Bola Tinubu

Bisi Akande ya ce wannan batu ya damu magoya bayan Tinubu, har suka roke shi da ya shiga tsakani domin shawo kansa.

Ya ce lokacin da ya gana da shugaba Tinubu, ya fada masa cewa wannan dama ce da Yarbawa ke da ita na karɓe mulkin Najeriya don haka ya yi haƙuri ya nemi takara.

Ya ce wannan magana da sauran kalaman da ya yi amfani da su wajen shawo kansa sun eazana Tinubu har ya kalle shi kamar yana fama da rashin lafiya.

Bola Tinubu na fama da ciwon ƙafa

Daga karshe, Bola Tinubu ya nuna damuwa kan matsalar ciwon gaɓoɓi da yake fama da shi musamman a ƙafarsa.

Tsohon gwamnan ya ci gaba da cewa:

"Ya tambaye ni, Baba, yanzu kana cewa in tsaya takara, ya zan yi da wannan ciwo na ƙafata?’ Na tabbatar masa da cewa ya tafi ya yi magani, cikin watanni shida zai warke."

Kara karanta wannan

'Na samu lafiya,' Buhari ya fadi kalubalen da ya fuskanta a lokacin mulkinsa

Yadda aka tilastawa Tinubu takara a 2023

A wani labarin, kun ji cewa dattijon ƙasa, Bisi Akande ya bayyana kalaman da ya yi amfani da su wajen shawo kan Bola Tinubu ya nemi takarar shugaban ƙasa.

Akande ya tabbatar da cewa da farko Tinubu ba shi da sha'awar tsayawa takara amma bayan ya gana da shi, ya samu nasarar shawo kansa da al'adun Yarbawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel