Ministan Tinubu Zai Ajiye Mukaminsa, Zai Tsaya Takarar Gwamnan Osun? APC Ta Magantu
- APC ta yi karin haske yayin da aka ga bullar wasu fastocin ministan tattalin arzikin ruwa na neman takarar gwamnan Osun
- Daraktan yada labaran APC, Mista Kola Olabisi ya ce fastocin da ake yadawa a jihar ba su da alaka da ministan, Gboyega Oyetola
- A cewar Olabisi, ministan Shugaba Bola Tinubu, Mista Otetola bai fito ya nuna sha'awar neman takarar gwamnan jihar Osun ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - A ranar Laraba, jam'iyyar APC a jihar Osun ta warware rudanin da aka samu game da fastocin yakin neman zaben Gboyega Oyetola da suka karade jihar.
A jikin fastocin, an nuna cewa Oyetola, wanda shi ne ministan tattalin arzikin ruwa a gwamnatin Bola Tinubu ya fito takarar gwamnan Osun.

Asali: Twitter
APC ta karyata takarar ministan Tinubu
A cikin sanarwar da daraktan yada labaran APC na Osun, Mista Kola Olabisi ya fitar, jam'iyyar ta nemi 'yan jihar da su yi watsi da wadannan fastoci, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Kola Olabisi ya bayyana cewa bugawa da lika fastocin a sassan jihar aikin 'yan adawa ne da ke son ruguza tsarin jam'iyyar APC a Osun.
Daraktan yada labaran ya ce:
"Mun san daga ina wadannan fastocin bogin suka fito kuma mun san manufarsu ita ce kawo rudani a jam'iyyarmu da nufin cimma wata manufarsu.
"Abin takaicinmu a matsayin jam'iyyar adawa a jihar Osun a yau shi ne wadanda ke yada wanann abu sun ki fitowa su bayyana kansu, sai 'yar labe kawai suka iya."
APC ta zargi 'yan adawa da yada fastoci
Mista Olabisi ya ce jagoran jam'iyyar APC a Osun wanda shi ne tsohon gwamnan jihar, bai buga wata fasta ta neman takarar kujera ba.
"Bai buga ko lika fastoci a sassan jihar da sunan neman wata kujera ba, sabanin karairayin da ke kunshe a cikin wadannan fastoci.
"Ministan harkokin tattalin arzikin ruwa bai yi da kansa ba kuma bai sa wani ya yi a madadinsa ba, walau don siyasa ko don wata manufa."
- Mista Olabisi.
Vanguard ta rahoto daraktan yada labaran ya ce buga fastar da likata wata hanyar yada jita jita ce da wasu 'yan adawar siyasa suka kirkiro domin tayar da zaune tsaye a APC.
An nemi Oyetola ya sake takarar gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar IPSC da ke goyon bayan jam'iyyar APC ta bukaci Gboyega Oyetola ya sake dawowa ya nemi takarar gwamnan jihar Osun.
A cewar shugabannin kunguyar IPSC, Oyetola ne kaɗai zai nemi takara a zauna lafiya a jam'iyyar APC reshen jihar Osun saboda shi ne jagoranta.
Asali: Legit.ng