Abincin Wasu Ya Kare: Gwamna Ya Fatattaki Kwamishinoni 5, An Maye Gurbinsu Nan Take

Abincin Wasu Ya Kare: Gwamna Ya Fatattaki Kwamishinoni 5, An Maye Gurbinsu Nan Take

  • Gwamnatin Jihar Filato ta sallami kwamishinoni biyar daga majalisar zartarwa, inda aka nada sababbi domin maye gurbinsu ba tare da bata lokaci ba
  • Kwamishinonin da abin ya shafa sun hada da na Kasuwanci da Masana’antu, Kimiyya da Fasaha, Matasa da Wasanni, Tattalin Arziki, da Yawon Bude Ido
  • Gwamna Caleb Mutfwang ya nada sababbin kwamishinoni daga kananan hukumomi daban-daban, ya yi wa tsofaffin kwamishinonin fatan alheri a aikinsu na gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jos, Plateau - Gwamnatin Jihar Filato ta amince da sallamar wasu mambobin PDP majalisar zartarwa ta jiha tare da nada sababbi domin maye gurbin su nan take.

Gwamna Caleb Mutfwang shi ya dauki wannan mataki domin kawo sababbin jini a harkokin gwamnatin jihar.

Gwamna ya kori kwamishinoni 5 a Plateau
Gwamna Caleb Mutfwang ya kori kwamishinoni 5 a Plateau inda ya maye gurbinsu nan take. Hoto: Caleb Mutfwang.
Asali: Twitter

Gwamna Caleb ya gana da Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Yaki da talauci: Gwamnan Jigawa ya raba tallafin kudi ta katin ATM

Vanguard ta ruwaito cewa kwamishinonin da aka sallama sun hada da Sule Musa na Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu da Obed Goselle na Kimiyya da Fasaha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne makwanni bayan ganawar Gwamna Caleb Mutfwang da Bola Tinubu inda ya ce an samu gagarumin ci gaba a yanayin tsaro a jihar daga Janairu zuwa Disambar 2024.

Gwamnan ya ce shugaba Bola Tinubu ya bayar da gudunmawa sosai kuma yana da jajircewa wajen inganta tsaro a jihar.

Kwamishinoni da aka sallama a Plateau

Sauran kwamishinonin da aka kora akwai Noel Nkup na Matasa da Wasanni da Chrysantus Dawam na Tsare-tsaren Tattalin Arziki da Jamila Tukur na Yawon Bude Ido.

Sai dai nan take Gwamna Caleb ya fitar da wasu sunaye a matsayin kwamishinoni domin maye gurbin wadanda aka sallama daga kujerunsu.

Sababbin kwamishinoni da aka nada a Plateau

Daga cikin sababbin kwamishinonin da aka nada akwai Sunday Alex daga Karamar Hukumar Bassa da Joyce Ramnap daga Langtang ta Kudu.

Kara karanta wannan

An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

Sai kuma Sylvanus Dongtoe daga Shendam da Nicholas Baamlong daga Qua’an Pam da Cornelius Doeyok daga Qua’an.

Gwamnan daga bisani ya yi wa tsoffin kwamishinonin godiya kan gudunmawar da suka bayar da kuma fatan alheri, cewar Tribune.

Plateau: Kungiyar APC tana zawarcin Gwamna Caleb

Kun ji cewa Ƙungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta sake gayyatar gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya fice daga PDP ya shiga jam’iyyarta domin samun karin damar ci gaba.

Sanarwar da Saleh Zazzaga ya fitar ta bayyana cewa shiga APC zai ba Mutfwang damar jagorantar jam’iyyar a jihar Filato gabanin taron jam’iyyar.

Ƙungiyar ta jaddada cewa shiga APC zai kara haɗin kai tsakanin Mutfwang da shugaba Bola Tinubu, tare da tabbatar da cigaban jihar Filato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel