Matasa Sun Ajiye Tinubu, Sun Fara Kiran Rahama Sadau Ta Fito Takarar Shugabar Kasa
- Wani matashi ya bukaci 'yar wasar fim, Rahama Sadau ta fito takarar shugabar Najeriya a 2027 domin shahararta da tarin masoya
- Wasu sun goyi bayan wannan kiran yayin da wasu suka nuna ko kusa ba ta cancanci neman kujerar shugaba Bola Tinubu ba
- Wannan na zuwa ne yayin da Rahama ta wallafa "Salaam" a soshiyal midiya, wanda ya sa mutane sama da 2,200 suka yi martani
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Soshiyal midiya ta dauki zafi da wani matashi ya nemi fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta fito takarar shugabar Najeriya a 2027.
An nemi Rahama Sadau ta gwabza da Shugaba Bola Tinubu a 2027 ne yayin da jarumar ta wallafa wani sako da ya ja hankalin dubunnan mutane.

Asali: Twitter
Rahama Sadau ta jawo ce-ce-ku-ce
Da misalin karfe 12:41 na safiyar ranar Laraba, Rahama Sadau ya yi sallama a shafinta na Facebook, wanda ya jawo martanin sama da mutane 2,200.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan wannan sallamar da ta yi, babu wani da jarumar ta rubuta sai alamar idanuwa, amma hakan bai hana dubunnan masoyanta yin magana ba.
Ga abin da jarumar ta ce:
"Salaam…👀"
Haruffa shida da alamomin rubutu uku da alamar ido da jarumar ta rubuta, sun yi tasiri a zukutan masoyanta da har ya kai ga an tafka muhawara.
Ana so Rahama ta fito takarar shugaban kasa
Daga cikin wadanda suka yi martani, akwai, Hamza M Kankia, wanda dan asalin jihar Katsina ne da ya nemi jaruma Rahama ta fito takarar shugaban kasa.
Hamza Kankia ya ce ya ga dacewar 'yar wasar Hausan ta nemi kujerar Shugaba Tinubu a zaben mai zuwa saboda shahara da tarin masoyan da take da su.
Ga abin da Hamza ya ce:
"Kina da tarin masoya, kawai ki fito takarar shugabar kasar Najeriya."
Mutane hudu sun yi martani ciki har da Rahama Sadau wacce ta sanya alamar 'aljanun dariya', yayin da wani Ishaq Babangida Abubakar ya ce:
"Za mu zabe ki, sosai, kina da kirki Rahama."
Sai dai Kabiru AG ya yi wa Hamza M Kankia martani da cewa lallai Rahama za ta lashe zaben idan na soshiyal midiya ne, "musamman ma ace da Ado Gwanja za ta yi takara."
Muhammad Sulaiman Jariri dai ya gargadi Hamza, da ya rufawa Rahama asiri, kar wasu su ji wannan maganar, a tono wani abu nata da ba a sani ba.
Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya nada Rahama Sadau mukami a kwamitin shirin saka hannun jari na kere-kere.
Mutane 2,200 sun yiwa Rahama martani
Kamar yadda muka ambata a farko, sallamar da mai shirya finafinan ta rubuta ta jawo martanin sama da mutane dubu 2,200, wanda muka zakulo wasu daga ciki:
Maryam Ameenu:
"Kam bala'i in miniti 3 kin samu sama da martani 400.
"Sannu kin ji Rahama Sadau 'yar sababi ❤️😅"
Abdulsalam Umar:
"A ba mu kudi hajiya 🤗🚶🏿"
Abdullahi Sabo Kibiya:
"Wa'alaikum Salam, gaskiya ina sonki sosai Rahmam. Ina son ki kamar na mutu."
Fatema Muhammad:
"Ni har yanzu mutane mamaki suke bani, sai kace ba sune shekarun baya suke zagi da nuna kiyayya ga Rahama Sadau ba, amma yanzu su ne ke bibiyarta. Lalle Tinubu ka yi aiki."
Rabiu Salafii:
"Ya hallata idan Rahama Sadau ta bani kudi na yi anfani dasu?
"Tambaya nake?
Ali Nuhu ne silar shigar Rahama Kannywood
A wani labarin, mun ruwaito cewa jaruma Rahama Sadau ta shaidawa duniya cewa fitaccen dan wasan Hausa, Ali Nuhu ne silar shigarta masana'antar Kannywood.
A wata hira da aka yi da ita, ta shaida cewa Ali Nuhu ya fara haduwa da ita ne a wani gidan Rawa a jihar Kaduna, ya ga dacewar ta fara fitowa a finafinan Hausa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng