Bayan Kiran El Rufa'i, Peter Obi Ya Ce Ya Yarda da Hadakar 'Yan Adawa a 2027
- Bayan wani kira da tsohon gwamnan jihar Kaduna ya yi a Abuja, Peter Obi ya yi karin haske kan kulla kawance da 'yan adawa a zaben 2027
- Tsohon dan takara a jam'iyyar LP, ya ce an yi wa kalamansa mummunar fassara kan batun haɗin kai domin kayar da jam'iyyar APC a 2027
- Peter Obi ya jaddada cewa dole ne haɗin gwiwa ta zama domin amfanin ’yan Najeriya da ceto su daga halin da suke ciki kafin ya shiga cikinta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya musanta cewa yana adawa da haɗin gwiwar 'yan adawa domin kayar da APC a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
A baya, Obi ya bayyana a wani taro da aka gudanar a Abuja cewa ba ya maraba da ƙoƙarin wasu jagororin adawa na haɗa kai domin kwace mulki a 2027.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a ranar Talata, ya fitar da wata sanarwa ta hannun mai magana da yawunsa, Ibrahim Umar, inda ya ce an yi wa kalamansa mummunar fassara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi: “Ba na adawa da haɗin gwiwa”
Peter Obi ya ce wasu kafafen yaɗa labarai sun fassara maganarsa ba daidai ba, ya ce yana goyon bayan haɗin gwiwa, amma ba domin kwace mulki kawai ba, sai saboda inganta Najeriya.
"Na lura cewa an yi wa tattaunawa ta fassara mara kyau, wadda ke ƙoƙarin bayyana ni tamkar wanda ba ya goyon bayan haɗin gwiwa.
"Bari in fayyace matsayina: Ba na adawa da haɗin gwiwa. A gaskiya, ina goyon bayanta,

Kara karanta wannan
'Babban abu na shirin faruwa': Martanin yan Najeriya da Peter Obi ya ziyarci jigon APC a Kano
Amma ba domin kwace mulki kawai ba, sai idan za a yi sa saboda inganta rayuwar ’yan Najeriya."
- Peter Obi
Ya jaddada cewa ko wane irin shiri na siyasa dole ne ya fi mayar da hankali kan al’ummar ƙasa, ba wai kawai batun kwace mulki ba.
Obi ya fadi sharadin hadin gwiwa
Peter Obi ya ce dole ne a mayar da hankali kan inganta rayuwar talakawa a kowane shiri na haɗin gwiwa domin kayar da jam'iyyar APC.
Ya ce siyasa ba ta da amfani idan ba za ta magance matsalolin rayuwa kamar kiwon lafiya, ilimi da talauci ba.
"A tarihin Najeriya, mun sha ganin haɗin gwiwa da ƙungiyoyi ke yi ba tare da wata manufa mai kyau ba.
"Wadannan haɗin kan ba su tsinana wa talakawa komai ba, sai dai ƙara jefa su cikin mawuyacin hali. Wannan ne nake ƙin amincewa da shi."
- Peter Obi
Obi ya ce dole ne hadaka ta zama mai ma’ana, kuma dole ne ta kasance mai manufar kawo sauyi ga ƙasa, ba wai kawai neman mulki ba.
APC ta yi martani ga Nasir El-Rufa'i
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi martani ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i kan kiran 'yan adawa su hada kai.
Haka zalika jam'iyyar APC ta ce bai dace El-Rufa'i ya yi kalaman ba kasancewar yana da damar isar da matsalar da yake gani ga jam'iyyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng