'Dan Majalisar Tarayya na Kano na Tsaka Mai Wuya, Yunƙurin Tsige Shi Ya Kara Tsananta
- Yunƙurin mutanen mazaɓar Dala a Kano na dawo da ɗan Majalisarsu na tarayya, Hon. Aliyu Sani Madaki ya kara tsananta a ƴan kwanakin nan
- An ruwaito cewa masu ruwa da tsaki a yankin na Dala sun yi taro kan lamarin kuma sun lashi takobin yi wa ɗan Majalisar tarayyar kiranye
- Kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Waiya da ɗan majalisar dokoki na Dala ne ke jagorantar raba Madakin Gini da kujerarsa bisa tanadin doka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Yunƙurin yi wa mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar wakilai, Aliyu Sani Madakin Gini, kiranye ya ƙara zafafa a mazaɓarsa watau Dala da ke Kano.
Rahotanni sun nuna cewa waɗanda ke jagorantar wannan yunƙuri sun haɗa da shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin Kano, Hon. Lawan Hussaini Chediyar Yar Gurasa.

Asali: Facebook
Sai kuma kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifin da ɗan Majalisar NNPP ya aikata
Jiga-jigan NNPP a ƙaramar hukumar Dala sun zargi Madakin Gini da cin amanar jam’iyya da kuma haɗa kai da ƴan adawa.
Sun zargi Ɗan majalisarsu na tarayya da cin amanar jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso da kuma tafiyar Kwankwasiyya.
A wani taron masu ruwa da tsaki, kwamishinan da ɗan majalisar da ke wakiltar Dala a Majalisar Dokokin Kano sun sha alwashin tabbatar da an yi wa Madakin Gini kiranye.
Wannan na zuwa ne bayan da Madakin Gini ya sanar da ficewarsa daga tafiyar Kwankwasiyya, duk da cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar NNPP.
Madakin Gini, wanda tsohon jigo ne a tafiyar Kwankwasiyya, an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai daga mazabar tarayya ta Dala a 2023 a inuwar NNPP.
Sai dai kuma daga baya ya nisanta kansa da Kwankwaso da tafiyarsa tare da hada kai da wani bangare na NNPP karkashin jagorancin Cif Boniface Aniebonam.
Shirin dawo da Hon. Ali Madakin Gini gida
Yayin da yake jawabi a taron, Ibrahim Waiya ya tabbatar wa mahalarta taron cewa za a cika dukkan sharuddan da doka ta gindaya.
Ya ce za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) domin tabbatar da nasarar aikin dawo da ɗan Majalisar gida.
A nasa bangaren, Lawan Hussaini Chediyar Yar Gurasa ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda Madakin Gini, wanda Kwankwasiyya ta yi wa riga da wando ya haɗe da APC.
Kokarin jin ta bakin Hon. Madakin Gini bai samu nasara ba, domin bai amsa kiran waya ba.
Tsagin NNPP ya yi fatali da barazanar
Sai dai shugaban NNPP ta Kano na tsagin da ke adawa da gwamnati, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa, ya yi watsi da wannan yunƙuri, yana mai cewa abin dariya ne.
Mas'ud Doguwa ya jaddada cewa kundin tsarin mulki ya shimfiɗa cikakkiyar hanya da dole ne a bi wajen tsige ɗan majalisa daga mazabarsa.

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
Ya kuma ce Ibrahim Waiya da Chediyar Yar Gurasa ba su da ƙarfin cika waɗannan sharuɗɗa, sannan ya buƙaci ‘yan NNPP su yi watsi da barazanar.
Ana fara gangamin haɗa Kwankwaso da Ganduje
Kun ji cewa wasu ƴan siyasa a jihar Kano sun fara yunkurin sasanta tsofaffin gwamnoni, Rabiu Musa Kwankwaso da Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Waɗannan ƴan siyasa na ganin rashin jituwar Kwankwaso da Ganduje ba ƙaramar illa take yi wa Kano ba don haka suka fara gangamin sulhu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng