Sukar APC: Shehu Sani Ya Yi Wa El Rufai Wankin Babban Bargo
- Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya tuna baya kan taƙun saƙar da yake yi da Malam Nasir El-Rufai wanda ya yi gwamna a jihar Kaduna
- Shehu Sani ya bayyana tohon gwamnan na jihar Kaduna a matsayin mutum wanda baya jurewa shan suka daga wajen waɗanda suke adawa da shi
- Taohon sanatan ya zargi El-Rufai da taka wanda ya ga dama a lokacin da yake cikin gwamnati amma yanzu kiran da koma kan turbar mutunta dimokuraɗiyya
- Sanata Shehu Sani ya nuna cewa tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ya na sukar APC ne saboda ya kasa samun muƙamin a cikin gwamnatin Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Tsohon sanatan da ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya soki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.
Shehu Sani ya caccaki Nasir El-Rufai ne kan wasu kalaman da ya yi a kan jam'iyyar APC a cikin ƴan kwanakin nan.
Tsohon sanatan ya yi martani ga El-Rufai ne a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasir El-Rufai ya caccaki APC
A cewar Sani, El-Rufai ya yi kama karya a lokacin da yake kan mulki, amma yanzu yana son a dawo kan turbar bin dimokuraɗiyya bayan ya bar ofis.
Idan ba a manta ba dai a wani taro da aka gudanar ranar Litinin a Abuja, El-Rufai ya zargi jam’iyyarsa ta APC da watsi da tsare-tsarenta na asali da kuma samar da shugabanci mara inganci.
Wane martani Shehu Sani ya yi wa El-Rufai
Tsohon sanatan ya bayyana El-Rufai a matsayin mutum wanda bai sukar wani abu, sai bayan ya rabu da shi.
Shehu Sani ya bayyana El-Rufai a matsayin mutumin da har yanzu yake jin zafi saboda bai samu karɓuwa ba, a gwamnatin APC.
"Mutumin da ke da tarihin rashin haƙuri da ƴan adawa da kuma rashin jurewa suka, ba shi da wata ƙimar da zai hau kan mumbarin dimokuraɗiyya ya jawo hankali kan shugabanci mai kyau."
"Idan Nasir El-Rufai yana cikin Keke Napep, zai kira ta da Lamborghini, idan aka fitar da shi daga Lamborghini, zai kira ta Keke Napep. Ya zagi ƴan adawa yayin da yake kan mulki, amma yanzu ya koma wajensu."
A cewarsa, gwamnatin Tinubu a yau tana cike da jahilai ne saboda sun ƙi ba Farfesa Nasiru muƙami.
Shehu Sani ya kuma zargi El-Rufai da barin tarkace a Kaduna amma yanzu yana wa’azin tsafta a Najeriya.
El-Rufai ya magantu kan barin APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya musanta rahotannin da ke cewa ya fara tattara komatsansa domin ficewa daga APC.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa bai da shirin ficewa daga APC, amma yana matsa mata lamba ne domin kawai ta gyara kura-kuran da take yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng