'Su Bar Kujerunsu': Atiku ga Yan Siyasa da Ke Sauya Sheka, Ya Fadi Hanyoyin Gyara Dimukraɗiyya
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki yan siyasa game da sauya sheka zuwa wasu jam'iyyu
- Atiku Abubakar ya ce ya kamata ‘yan siyasa da suka bar jam’iyyarsu suka koma wata su rasa kujerunsu don tabbatar da karfin dimukraɗiyya
- Ya jaddada cewa dimukuradiyya ba za ta dore ba idan jam’iyyun siyasa ba su kasance masu karfi da tsari ba, musamman a matsayin adawa
- Ya yi kira ga gyaran bangaren shari’a don magance matsalolin da suka dabaibaye tsarin zaben Najeriya da kuma tabbatar da hukunta masu karya dokokin jam’iyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukaci kawo sauyi game da sauya shekar yan siyasa.
Atiku ya ce ya kamata a haramta wa zababbun shugabanni sauya sheka daga jam’iyya daya zuwa wata yayin mulkinsu.

Asali: Facebook
El-Rufai ya caccaki salon mulkin APC
Atiku ya bayyana haka ne a jiya Litinin 27 ga watan Janairun 2025 yayin watmni taron kasa a Abuja, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce akwai bukatar ceto dimukuradiyya a Najeriya yana mai kira ga jam’iyyun adawa su haɗa kai.
El-Rufai ya yi gargadin cewa ana hasashen kashi 75% na masu kada kuri’a sun yanke shawarar ba za su fita zabe ba a 2027.
Tsohon gwamnan ya ce APC ta kauce wa manufofinta na farko kuma dole ne a dawo da martabar siyasar Najeriya.
Atiku ya caccaki yan siyasa kan sauya sheka
Atiku ya bayyana muhimman matakai guda biyar don karfafa dimukuradiyya, ciki har da gyaram shari’a da karfafa dokokin jam’iyyu.
Ya ce dole ne a sanya tsauraran hukunci ga wadanda suka saba dokokin jam’iyya, inda ya yi kira ga zababbun shugabanni masu sauya sheka su bar kujerunsu.
Atiku ya ce rashin da’a da son zuciya daga wasu ‘yan siyasa ya sanya dimukuradiyya a Najeriya ke fuskantar barazana mai tsanani a halin yanzu.
Atiku ya bukaci kawo gyara a bangaren shari'a
Tsohon dan takarar shugaban kasa ya yi suka kan yadda shari’a ke nuna goyon baya ga karya doka da sauya sheka ba tare da tsoron hukunci ba, yana mai kira da gyaran lamarin, cewar Channels TV.
Daga bisani, Atiku ya koka kan yadda shari’ar Najeriya ke canzawa daga kare zabin masu kada kuri’a zuwa kafa shugabanni bisa wasu dalilai maimakon muradun jama’a.
Atiku ya zargi Tinubu da saye yan adawa
A baya, mun ba ku labarin cewa Atiku Abubakar ya yi gargadin cewa Najeriya na iya rasa dimukiradiyyar da take tutiya da ita idan aka ci gaba da tafiya a haka.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya zargi gwamnatin APC da amfani da kudi wajen jan ra'ayin shugabannin jam'iyyun adawa.
Atiku ya bayyana cewa ya yi gwagwarmaya tsawon shekaru 30, kuma an sha yin yunkurin kashe shi, yana tsallake rijiya da baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng