Rigima Sabuwa: Kwamishinan Abba Ya Fara Shirin Yi Wa Dan Majalisar NNPP Kiranye

Rigima Sabuwa: Kwamishinan Abba Ya Fara Shirin Yi Wa Dan Majalisar NNPP Kiranye

  • Watakila kujerar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Dala daga jihar Kano, Ali Sani Madakin Gini, za ta fuskanci barazana
  • Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kiran da a yi wa ɗan majalisar kiranye
  • Ya nuna cewa bai kamata ɗan majalisar na jam'iyyar ya ci gaba da zama a kan kujerar ba saboda ba ya tare da mutanen da suka zaɓe shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira da a yi wa Hon. Ali Sani Madakin Gini kiranye daga majalisar wakilai.

Kwamishinan ya zargi Ali Sani Madakin Gini da gazawa wajen wakiltar al’ummar mazaɓar Dala yadda ya kamata a majalisar wakilai.

Za a yi wa Ali Sani Madakin Gini kiranye a Kano
An shirin yi wa Ali Sani Madakin Gini kiranye daga majalisar wakilai Hoto: Rufai Mohd Tofa, Kano State Ministry of Information and Internal Affairs
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa kwamishinan ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar NNPP a ƙaramar hukumar Dala.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa ake son yi wa ɗan majalisar NNPP kiranye?

Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana rashin gamsuwarsa kan kamun ludayin wakilcin Madakin Gini, yana mai cewa rashin jajircewarsa kan muradun mutanen mazaɓarsa ya sa dole ne a yi masa kiranye daga majalisa.

“Mutanen ƙaramar hukumar Dala sun cancanci samun wakilci mai kyau. Yin kiranye ga Hon. Madakin Gini abu ne da ya kamata domin ba ya kare muradun al’ummarmu."

- Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya

Kwamishinan ya jaddada muhimmancin siyasar ƙaramar hukumar Dala, ya nuna cewa tana da mafi yawan kwamishinoni a cikin majalisar zartarwar jihar Kano da kuma shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano.

Ibrahim Abdullahi Waiya ya yi zargin cewa ayyukan Madakin Gini sun nuna rashin jajircewa ga mutanen da suka zaɓe shi, rahoton Daily Post ya tabbatar.

“Madakin Gini ya bayyana a fili cewa ba ya tare da mutanen da suka yi ƙoƙarin ganin ya samu wannan kujera. Saboda haka, babu dalilin da zai ci gaba da zama a wannan muƙami alhalin ba ya kare muradun mutanen Dala."

Kara karanta wannan

Zargin neman cin hanci daga jami'o'i: Dan majalisa ya fadi yadda abubuwa suka kaya

"Idan shugabannin jam’iyya sun yarda, a shirye nake na fara aiwatar da shirin yi masa kiranye."

- Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya

Taron ya samu halartar fitattun mutane, ciki har da Alhaji Lawan Husaini Dala, shugaban NNPP reshen Dala; Alhaji Dayyab Ahmad Maiturare, kwamishinan muhalli na jihar Kano, Hon. Suraj Kwankwaso da sauransu.

Madakin Gini ya fice daga Kwankwasiyya

Idan ba a manta ba dai Madakin Gini ya bayyana ficewarsa daga tafiyar Kwankwasiyya a shekarar da ta gabata, amma bai yi murabus daga jam’iyyar NNPP ba.

Ya bayyana niyyarsa ta kafa sabuwar tafiya, bayan da ya nuna gamsuwa kan yadda ake gudanar da tafiyar Kwankwasiyya.

Jafar Jafar ya soki Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen ɗan jarida, Jafar Jafar ya nuna rashin gamsuwarsa kan shirin rabon awaki da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar.

Jafar Jafar ya nuna cewa bai kamata Gwamna Abba ya fito da kansa ya riƙa rabon awakin ga matan Karkara ba.

Kara karanta wannan

"Ana saye ra'ayin 'yan adawa da N50m": Atiku ya tona asirin gwamnatin Tinubu

Ɗan jaridar ya bayyana cewa rabon ƙananan abubuwa kamar su ba da awakai, aiki ne da ya kamata gwamnan ya bar wa shugabannin ƙananan hukumomi su yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng