Mawaki Rarara Ya Rikita Taro da Gwamna Ya Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Katsina
- Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Katsina
- A yayin taron, Ganduje ya karbi sama da mutane 40,000 da suka sauya sheka zuwa APC ciki har da tsohon shugaban jam'iyyar PDP
- Gwamna Dikko Radda ya yi alƙawarin gudanar da zaɓen ciyamomi mai inganci, tare da fatan jama'ar Katsina za su zabi APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen 'yan takarar ciyaman na jam'iyyar a jihar Katsina.
Taron ya samu sauyin sheƙar 'yan adawa sama da 40,000 daga jam’iyyun siyasa daban-daban zuwa APC a jihar Katsina.

Asali: Facebook
Kakakin gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya marabci jiga-jigan PDP zuwa APC
Ibrahim Kaula ya ce taron da aka gudanar a ƙaramar hukumar Ingawa ya samu sauyin sheƙar tsohon shugaban PDP na jihar, Alhaji Rabiu Gambo Bakori.
Ya ce wasu fitattun ‘yan siyasa da suka sauya sheƙa sun haɗa da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar Accord, Isah Hamisu Dandume, da Yakubu Idris Danchafa.
Ganduje ya bayyana cewa jajircewar gwamnatin APC wajen inganta rayuwar al'umma ita ce ta ja hankalin waɗannan manyan ‘yan siyasa zuwa jam’iyyar.
Ya tabbatar wa masu sauya sheƙar cewa za su sami kulawa da damarmaki iri ɗaya kamar sauran mambobin jam’iyyar APC.
Radda ya nemi a zabi 'yan takarar APC
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya tabbatar da kudirin gwamnati na gudanar da zaɓuka masu inganci da suka dace da muradin jama'a.
Gwamnan ya ƙarfafa masu zaɓe da su mara wa ‘yan takarar APC baya a zaɓen ƙananan hukumomi na watan Fabrairu da na 2027.
Ya ce gwamnatin APC za ta ci gaba da aiwatar da manufofinta domin kyautata rayuwar jama’ar jihar Katsina.
Dalilin sauya shekarar 'yan adawa a Katsina
Alhaji Rabiu Gambo Bakori, wanda ya wakilci masu sauya sheƙar, ya ce kyakkyawan shugabancin Gwamna Radda ne ya jawo hankalinsu su shiga APC.
Ya jaddada aniyarsu ta yin aiki tare da gwamnan don sake farfaɗo da jihar Katsina tare da kawo cigaba mai ɗorewa.
Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyya, masu ruwa da tsaki da masu zaɓe daga sassa daban-daban na jihar Katsina.
Wadanda suka halarta sun haɗa da Alhaji Ibrahim Kabir Masari, mataimakin shugaban APC na ƙasa da tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shehu Shema, da sauransu.
Mawaki Rarara ya rikita taro a Katsina
Fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara ya rikita taron yakin neman zaben 'yan takarar APC da aka gudanar a Ingawa, jihar Katsina.
Rarara da tawagarsa, ciki har da mawaki kuma jarumi Baban Chinedu da wasu mawaka da jaruman fim sun nishadantar da mahalarta taron.
Taron ya dauki shewa da kururuwar mutane a lokacin da mawaki Rarara ya fara rera wakar da ya yiwa Gwamna Radda mai taken "Gwagwaren Katsina - Fari Dogo."
Kalli bidiyon a nan kasa:
Asali: Legit.ng