'Neman Gwamna ba Zunubi ba ne': Kakakin Majalisa da Aka Tsige kan Dalilin Taso Shi a Gaba
- Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Legas, Mudashiru Obasa, ya bayyana dalilin da ya sa yake fuskantar matsaloli a jihar
- Hon. Obasa ya ce ana zargin yana da sha’awar gwamna ne kuma hakan ba laifi ba ne tun da tsarin dimukraɗiyya ake bi a Najeriya
- Dan siyasar ya musanta cewa yana neman kujerar gwamna, amma ya jaddada cancanta da kwarewarsa a matsayin mai jagorancin jihar
- Ya ce cire shi daga ofis ba bisa ka’ida aka yi ba, kuma har yanzu ya kasance shugaban majalisa a hukumance
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ikeja Lagos - Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Legas, Mudashiru Obasa, ya ce neman kujerar gwamna ba laifi ba ne.
Hon. Obasa ya koka kan yadda ake cire shi daga muƙaminsa ba bisa ka'ida ba inda ya ce an saba doka ta kowace hanya.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/df5dce189e8a4d8d.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan
![Tsoohn Kakakin Majalisa ya soki masu neman ganin bayansa a Lagos Tsoohn Kakakin Majalisa ya soki masu neman ganin bayansa a Lagos](https://cdn.legit.ng/images/1120/23491049332efc63.jpeg?v=1)
Asali: Original
Tinubu ya taka rawa kan dambarwar Majalisar Lagos
Obasa ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Ikeja, babban birnin jihar, bayan dawowarsa daga kasashen waje, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin rigimar, Shugaba Bola Tinubu ya yi kokarin shawo kan rikicin majalisar dokokin jihar Legas kafin tsige tsohon Kakakin Majalisar, Mudashiru Obasa.
Ana hasashen cewa Mudashiru Obasa ya rasa kujerarsa ne sakamakon zargin almundahana da rashin biyayya ga jagororin jam’iyyar APC.
Ana zargin cewa maganganu masu cike da girman kai da ya yi a lokacin gabatar da kasafin kudin 2025 na jihar Legas na cikin dalilan tsige shi.
Da aka tambaye shi ko cire shi daga ofis yana da nasaba da burinsa na zama gwamna, sai ya ce:
"Neman zama gwamna ba laifi ba ne."
Hon. Obasa ya bugi kirji kan takarar gwamna
A shekarar 2024, Obasa ya ce tsoffin gwamnonin Legas ba su fi shi cancanta ba, yayin da ake hasashen yana neman kujerar gwamna a 2027.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/5e9ba1098497f051.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe
Mudashiru Obasa ya musanta cewa yana son zama gwamna, amma ya ce yana da cancanta da gogewar jagorantar jihar Legas.
"Zama gwamna bai zama babban burina ba, amma hakan ba yana nufin cewa ba ni da shekaru ko gogewa da za su ba ni dama.
"Na taba fadar hakan a majalisa lokacin da aka gabatar da kasafin kudi, cewa ba na da tunanin zama gwamna, amma hakan ba yana nufin ba ni da cancanta."
- Mudashiru Obasa
Ya kuma ce majalisar dokokin Legas ba ta bi tsarin doka wajen tsige shi ba, kuma ya ce har yanzu shi ne shugaban majalisa a hukumance, cewar rahoton TheCable.
"A duk jihar Legas, babu wani shugaba da zai fito ya ce na tambaye shi ko ita cewa ina son zama gwamna."
- Mudashiru Obasa
Majalisa ta lissafo laifuffukan Hon. Obasa
Kun ji cewa Majalisar Dokokin Legas ta tsige Mudashiru Obasa bisa zarge-zargen almubazzaranci da dukiyar gwamnati da hada 'yan majalisa fada da junansu.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/63665015dc5825b8.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Mojisola Meranda, mai wakiltar Apapa I, ta maye gurbinsa,ta zama mace ta farko da ta dare kujerar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas.
Bayan tsige Obasa, jami’an tsaro sun kai dauki, inda suka kama wasu matasa dauke da kayan tsafe-tsafe da ke son shiga majalisar.
Asali: Legit.ng