Dan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Ya Shirya Ritaya, Zai Koma Malamin Makaranta
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya ce zai koma Onitsha ya zama malamin sakandare domin ya ƙarfafa ɗalibai
- Obi ya bayar da tallafin Naira miliyan 25 ga asibitin misiya da yake jihar Anambra, wanda ya ba su kyautarsa lokacin da yake gwamna
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra, Peter Obi ya yi bayani game da shirin da ya yiwa kansa na yin ritaya daga harkokin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ce zai koma Onitsha ya zama malamin sakandare.
Obi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke koyar da ɗaliban ajin ƙarshe na Dennis Memorial Grammar School, Onitsha, a bikin ranar ilimi ta duniya.

Asali: Twitter
Peter Obi ya shiga aji, ya koyar da yara
Dan takarar shugaban kasar ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Na zo wuce wa ta nan kawai sai na yanke shawarar yin bikin ranar ilimi ta duniya tare da ku, domin in ƙarfafa ku kan muhimmancin ilimi.”
A yayin da ya ce gobe ne makarantar za ta cika shekaru 100 da kafuwa, Peter Obi ya kuma ya ji daɗin kasancewa tare da ɗaliban don karfafa masu gwiwa.
“Na zo nan ne domin in karfafa muku gwiwa, babu karya da aka ce yara su ne manyan gobe, domin wasun ku ne za su rike mukamai, kamar gwamnoni da shugabanni nan gaba.
“Ilimi shi ne babban jari a rayuwarku. Idan kuna da ilimi, zaku iya cimma nasarori da dama. Ku dauki karatunku da muhimmanci."
- Peter Obi.
Peter Obi ya tuno da haduwarsa da Gowon
Tsohon gwamnan ya ba da labarin lokacin da Janar Yakubu Gowon ya ziyarci makarantar a shekarar 1970 lokacin da yana dalibi, amma daga baya ya zauna a tebur ɗaya da shi.

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
Ya ce:
“A wannan makarantar a shekarar 1970, ina tsaye a bakin kofa don na sarawa Janar Gowon da ya ziyarce mu, na shiga sahun sauran yara domin yi masa wakar maraba."
“Daga wannan makarantar, ilimi ya taimaka min wajen zama cikin manyan shugabanni. Wannan ne ya sa nake ƙarfafa ku kan muhimmancin ilimi,” a cewar Obi.
Peter Obi ya fadi shirinsa na yin ritaya
Peter Obi ya ce yana fatan yin ritaya a Onitsha domin ya koyar a makarantar sakandare don zama abin koyi da karfafa gwiwar yara su yi nasara a rayuwarsu.
"Ina fatan yin ritaya a nan Onitsha wata rana, kuma in dauki aikin koyarwa don karfafa gwiwar yara," inji Obi.
Ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan 25 ga wani asibitin misiya na Rex Universorum Charles Heerey, da ke Mmiata Anam, a jihar Anambra.
Ya miƙa tallafin ne ga Sista Mary Akabogu, shugabar ƙungiyar Immaculate Heart of Mary, wacce ke kula da asibitin.

Kara karanta wannan
'Ni kadai ke da iko': Gwamnan APC ya rikita zaman makoki, ya gargadi maciya amana
Obi ya tuna cewa lokacin da yake gwamna, ya miƙa kyautar asibitin ga kungiyar domin cigaba da gudanar da shi yadda ya dace.
Jami'an DSS sun kama Peter Obi?
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar LP, Peter Obi, ya musanta jita-jitar cewa hukumar DSS ta kama shi a birnin Abuja.
Obi ya ce labarin cewa an kama shi "karya ce tsagwaronta," yana mai jaddada cewa babu wani gaskiya a cikin rahoton.
Tsohon gwamnan Anambra ya tabbatar da cewa yana gida a Onitsha, tare da yin kira ga 'yan Najeriya su guji yada jita-jita marasa tushe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng