Atiku Ya Manta da Rashin Jituwa a Siyasa, Ya Jajanta da Yayan Gwamna Ya Rasu
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya tura sakon ta'azziya kan rashin dan uwan Gwamna Seyi Makinde
- Atiku ya jajanta tare da nuna takaici kan rasuwar babban yayansa mai suna Sunday Makinde a yau Juma'a
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP ya kuma mika ta'aziyyata ga dangin marigayin tare da yin addu'ar Allah ya ba su hakurin jure wannan babban rashi
- Hakan ya biyo bayan sanar da rasuwar marigayin wanda shi ne babban dan uwan gwamnan a yau Juma'a 24 ga watan Janairun 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya tura sakon ta'azziya ga Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Atiku ya jajanta wa gwamnan bayan rasuwar babban yayansa mai suna Injiniya Sunday Makinde a yau Juma'a 24 ga watan Janairun 2025.

Asali: Facebook
Yayan Gwamna Seyi Makinde ya kwanta dama
Atiku ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Juma'a 24 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan sakon ta'azziya na zuwa ne bayan Allah ya yi wa Sunday Makinde, yayan Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo rasuwa da daddare, wayewar garin yau Juma'a, 24 ga watan Janairu.
Ɗaya daga cikin ƙannensa ya bayyana cewa Injiniya Sunday Makinde ya rasu ba zato ba tsammani da misalin ƙarfe 3:20 na dare.
Tuni dai ƴan uwa da abokan arziki suka fara jimami da ta'aziyyar rashin yayan mai girma gwamna, wanda ya rasu ya bar ƴan uwa, 'ya'ya da jikoki.
Atiku ya tura sakon ta'azziya ga Seyi Makinde
A cikin sanarwar, Atiku ya ce ya shiga cikin alhini kan rasuwar tare da yi masa addu'ar samun rahama da sauran wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kuma mika ta'aziyyata ga dangin marigayin tare da addu'ar Allah ya ba su hakurin jure wannan babban rashi.
Daga bisani, ya yi addu'ar Allah ya jikansa da rahama, ya sanya shi cikin kwanciyar hankali da salama a rayuwar lahira.
Atiku ya yi addu'ar samun rahama ga marigayin
"Cikin alhini, ina mika ta’aziyyata ga Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, kan rasuwar babban yayansa, Sunday Makinde."
"Ina kuma mika ta’aziyyata ta musamman ga iyalan marigayin tare da yin addu’ar Allah ya ba su karfin hali da hakurin jure wannan babban rashi."
"Allah ya jikansa da rahama, ya sanya shi cikin kwanciyar hankali da salama a rayuwar lahira."
- Atiku Abubakar
Tsohon hadimin Atiku ya kwanta dama
Kun ji cewa hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Hon. Shima Ayati ya rasu a Makurdi bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ayati ya yi aiki tare da Atiku Abubakar a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo kuma ya jagoranci kwamitin tallafin Zaki Biam a 2003.
Marigayin dan asalin karamar hukumar Ukum ta jihar Benue, ya bar siyasa domin mayar da hankali kan kasuwancinsa.
Asali: Legit.ng