Tazarcen Trump a Wa'adi na 3: An Buga Muhawara a Majalisar Amurka

Tazarcen Trump a Wa'adi na 3: An Buga Muhawara a Majalisar Amurka

  • Dan majalisar dokokin kasar Amurka, Andy Ogles, ya gabatar da kudirin gyara tsarin mulki domin ba shugaba Donald Trump damar yin wa’adi na uku
  • Kudirin ya bukaci sauya gyaran dokar kasar da ta iyakance wa’adin shugabancin Amurka zuwa wa’adin mulki biyu kacal
  • Kudirin na fuskantar adawa daga ‘yan jam’iyyar Democrat, yayin da Trump ya nuna sha’awar yiwuwar wa’adi na uku a wasu lokutan baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Wani dan majalisar dokokin Amurka daga jam’iyyar Republican, Andy Ogles, ya gabatar da kudirin gyaran dokar kasa a ranar Alhamis.

Andy Ogles ya gabatar da kudirin ne da nufin bai wa shugabanni damar yin wa’adi na uku a ofishin shugaban kasa.

Trump
An fara maganar tazarcen shugaba Trump na 3. Hoto: Donald J. Trump
Asali: Getty Images

Rahoton CNBC ya ce Ogles ya bayyana cewa Shugaba Donald Trump ya cancanci karin lokaci domin gyara gazawar gwamnatin Biden da mayar da Amurka zuwa matsayinta a duniya.

Kara karanta wannan

Trump ya fara farautar baki, za a koro 'yan Najeriya mutane 5,144 gida

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudirin ya biyo bayan nadin Trump a matsayin shugaban kasa bayan samun nasara a zaben Amurka da ya gudana a 2024.

Gyaran doka domin kara wa’adin Trump

Andy Ogles, wanda yake wa’adi na biyu a majalisar dokokin Amurka, ya bayyana cewa ya kamata a gyara dokar da ta kayyade wa’adin shugabanci zuwa biyu.

Jaridar Express Tribune ta wallafa cewa Andy Ogles ya ce sauya dokar yana da muhimmanci domin bai wa Trump damar ci gaba da jagoranci.

“Trump ya nuna cewa shi ne kadai jagoran da zai iya fitar da kasar nan daga halin da ta shiga, domin haka dole ne mu samar masa da duk wata dama da zai bukata,”

- Andy Ogles

Dokar Amurka da aka kirkira a shekarar 1947, an amince da ita a shekarar 1951 domin hana sake maimaita mulki irin na shugaba Franklin Roosevelt da ya yi wa’adin mulki har guda hudu.

Kara karanta wannan

'Su bar kujerunsu': Atiku ga yan siyasa da ke sauya sheka, ya fadi hanyoyin gyara dimukraɗiyya

Kalubalen kudirin a majalisar dokoki

Kudirin gyaran dokar na Ogles ya zo ne bayan wani dan majalisar Democrat daga New York, Dan Goldman, ya gabatar da kudiri mai tabbatar da cewa dokar hana karin wa'adi na nan daram.

Dan Goldman ya kuma tabbatar da cewa ba za a ba shugaba Donald Trump damar wa’adi na uku ba.

Amma duk da haka, Ogles ya dage da cewa wannan kudiri nasa zai bai wa Trump damar ci gaba da jagoranci domin ci gaban kasa.

Tuni kudirin ya fara fuskantar cikas, musamman ganin cewa jam’iyyar Republican ba ta da rinjaye a majalisar wakilai, yayin da ake sa ran jam’iyyar Democrat za ta ki amincewa da shi.

Trump na son wa’adi na uku?

A yayin yakin neman zabensa, Trump ya nuna cewa yana goyon bayan gyaran dokar idan har hakan zai ba shi damar ci gaba da mulki.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

A karkashin haka ake ganin cewa Donald Trump zai iya goyon bayan dokar domin sake tsayawa takara a zaben Amurka mai zuwa.

Trump ya caccaki malamar coci

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Donald Trump ya caccaki wata malamar coci yayin da ake masa addu'ar samun nasara.

Legit ta ruwaito cewa malamar cocin ta roki Donald Trump ya sassauta dokar masu sauya jinsi da bakin haure, lamarin da ya fusata shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel