Gaskiya Ta Fito da Aka Fara Zargin Minista kuma Jigon APC da Shirin Yaƙar Tinubu a 2027
- Karamin ministan man fetur, Ekperikpo Ekpo ya musanta zargin cewa yana da hannu a wani shiri na hana Shugaba Bola Tinubu tazarce a 2027
- Ministan ya jaddada biyayyarsa ga APC mai mulki tare da yin bayanin dalilin da ya sa aka ga alaƙa ta ƙullu tsakaninsa da gwamnan Akwa Ibom
- Ya ce ya haɗa kai da Gwamna Umo Eno duk da ba jam'iyyarsu ɗaya ba saboda tabbatar da zaman lafiya da kawo ci gaba a jihar Akwa Ibom
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Karamin ministan albarkatun man fetur (Gas), Ekperikpo Ekpo, ya musanta zargin cewa yana da hannu a shirin yaƙar tazarcen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a 2027.
Ministan ya karyata zargin da aka ce Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya dauke shi aiki don hana Shugaba Bola Tinubu samun wa’adi na biyu.

Asali: Facebook
Ekpo ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ministan, Louis Ibah, ya fitar ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin minista na shirin yakar Tinubu
Ya ce zargin ministan ya haɗa kai da Gwamna Umo Eno don kifar da Tinubu a zaɓen 2027 ya fito ne daga wata kungiya mai neman suna a jihar Akwa Ibom.
An ruwato cewa ƙungiyar mai suna, "tawagar ƴan APC masu kishi a Akwa Ibom," ta tura sakon zargin ƙaramin ministan ga shugaban ƙasa.
Ministan ya musanta zargin da ake masa
Mista Ibah ya ce:
“Za mu iya musanta wannan zargi cewa Mista Ekpo yana da hannu a wani shiri na ruguza shirin tazarcen Shugaba Tinubu."
Ya bayyana zarge-zargen a matsayin “ƙarya” da kuma “abin dariya,” yana mai jaddada cewa Mista Ekpo na nan a matsayinsa na amintaccen ɗan APC.

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
A cewar ministan, Gwamna Eno yana jagorantar gwamnati mai ƙaunar zaman lafiya a jihar Akwa Ibom ba tare da tsoma baki a harkokin APC ba.
Mista Ibah ya ce jajircewa da sadaukarwar ƙaramin ministan fefur ga jam'iyyar APC da manufofinta yana nan daram, babu abin da ya sauya.
Yadda Ekpo ya taimaki APC a zaɓen 2023
“Babu shakka Ekperikpo Ekpo ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa Akwa Ibom Democratic Forum (ADF), wata ƙungiyar siyasa da ta haɗa ‘yan asalin Akwa Ibom, wanda ya taimaka sosai a nasarorin da APC ta samu a zaɓen 2023.
“Ƙoƙarinsa ne ya kai ga nasarar Shugaban Majalisar Dattijai da ƴan Majalisar Wakilai 2 a zaɓen 2023, tare da shugaban ƙaramar hukumar Essien Udim da kujerun kansiloli," in ji shi.
Ƙaramin ministan albarkatun man fetur. Mista Ekpo haifaffen ƙaramar hukumar Ika ce a jihar Akwa Ibom.
Ya taba yin aiki a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Ika da kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Abak ta tarayya.
A cewar sanarwar, jajircewar ministan ga zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Akwa Ibom ne ya sa yake haɗin kai da Gwamna Eno.
Ohanaeze ta amince Tinubu ya yi takwas
Kuna da labarin cewa ƙungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu ya yi tazarce zango na biyu a 2027.
Sai dai kungiyar ta roki mai girma shugaban ƙasa da ya yi amfani da karfin mulkinsa ya kawo ƙarshen ƙungiyar ƴan awaren IPOB a Kudu maso Gabas.
Asali: Legit.ng