Bayan Korar Mataimakin Shugaban PDP na Ƙasa, An Naɗa Wanda Zai Maye Gurbinsa

Bayan Korar Mataimakin Shugaban PDP na Ƙasa, An Naɗa Wanda Zai Maye Gurbinsa

  • Bayan sallamar mataimakin shugaban PDP na ƙasa (Kudu maso Gabas), shugbanni daga jihar Ebonyi sun zaɓi wanda zai maye gurbinsa
  • Jam'iyyar PDP reshen Ebonyi ta aika wasiƙa ɗauke da sunan wanda zai maye gurbin ga muƙaddashin shugaban PDP, Ambasada Umar Damagum
  • Tun farko dai shugabannin PDP na wata gunduma a jihar Ebonyi sun dakatar da Ali Odefa daga bisani suka kore shi daga jam'iyyar gaba ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ebonyi - Jam'iyyar PDP reshen jihar Ebonyi ta zabi wanda take so ya maye gurbin tsohon mataimakin shugaban PDP (yankin Kudu maso Gabas) na kasa, Ali Odefa.

PDP ta fara ƙoƙarin maye gurbin Odefa ne bayan ta kore shi daga jam'iyyar bisa zargin aikata wasu laifuffuka da suka haɗa da cin amana, wanda ya saɓawa dokokinta.

Tutar PDP.
PDP ta zabi wanda zai maye gurbin mataimakin shugaban jam'iyya na Kudu maso Gabas Hoto: OfficialPDP
Asali: Twitter

PDP ta naɗa wanda zai maye gurbin Odefa

Kara karanta wannan

PDP ta kama hanyar zama tarihi a Najeriya, an tono masu koƙarin kashe jam'iyyar

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, PDP a Ebonyi ta zabi shugaban matasa na yankin Kudu maso Gabas, Chidiebere Egwu a matsayin wanda zai maye gurbin Ali Odefa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata wasika da ta aika wa mukaddashin shugaban PDP na kasa, Umar Damagum, da shugaban kwamitin amintattu (BoT), Sanata Adolphus Wabara.

Wasiƙar ta bayyana cewa PDP ta Ebonyi ta zabi Mista Egwu a matsayin sabon mataimakin shugaban jam'iyya na kasa (Kudu maso Gabas) sakamakon korar Odefa.

Yadda aka kori mataimakin shugaban PDP

Idan ba ku manta ba babbar kotun tarayya da ke zama a Abakaliki ta tabbatar da dakatarwar farko da shugabannin PDP na gundumar Oguduokwor a karamar hukumar Onicha suka yi wa Odefa.

Bayan dakatar da shi, kwamitin ladabtarwa na Oguduokwor ya saurari zarge-zargen da ake yi wa Mista Odefa kuma ya bayar da shawarar a kore shi daga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Shugaba a APC ya yi zazzafan martani ga El Rufa'i kan hadaka da 'yan adawa

Hakan ya sa a ranar 12 ga Disamba, 2024, shugabannin PDP na gundumar Oguduokwor suka sanar da kora ta karshe ga Mista Odefa.

Shugabannin PDP sun rattaɓa hannu kan wasiƙa

A halin yanzu kuma shugabannin kam'iyyar PDP na jihar Ebonyi sun amince da zaben Mista Egwu a matsayin wanda zai maye gurbin Mista Odefa.

Daga cikin wadanda suka rattaba hannu kan takardar sun hada da tsohon muƙaddashin sakaren jam'iyya na ƙasa, Cif Onwe S. Onwe, da Sanata Paulinus Igwe Nwagu.

Sai kuma tsohon mataimakin shugaban matasan PDP na ƙasa, John Igboke, da tsohon ɗan takarar gwamnan Ebonyi a inuwar PDP, Paul Okorie.

Wasikar amincewa da zaben Mista Chidiebere Egwu ta isa ga mukaddashin shugaban jam’iyya na ƙasa, sakatare, da shugaban kwamitin amintattu (BoT).

Haka nan kuma an tura wasiƙar ga shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP kuma gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed.

APC na yunƙurin mayar da PDP kamar wani reshenta

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukuncin da ka iya karya Wike, ta tsige shugaban jam'iyyar PDP

A wani labarin, kun ji cewa tsohon kakakin PDP ya bayyana masu yunƙurin karya babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa ta yadda za ta zama tarihi a Najeriya.

Mista Kola Ologbodiyan ya yi zargin cewa shugabannin APC na da hannu dumu-dumu a rikicin cikin gidan da ya addabi PDP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262