Ina Aka Kwana kan Jita Jitar Haɗaka tsakanin SDP, El Rufai da Atiku? An Gano Gaskiya
- Shugaban jam’iyyar SDP, Alhaji Shehu Gabam, ya yi magana kan batun hadaka da Atiku Abubakar da tsohon gwamna, Nasir El-Rufai
- Gabam ya musanta batun yarjejeniya da tsohon dan takarar shugaban kasa da kuma El-Rufai kafin zaben 2027 da nufin yakar APC
- Shugaban SDP ya ce jam'iyyar ta himmatu wajen samar da ingantaccen shugabanci don inganta rayuwa da magance matsalolin mulki
- Wannan na zuwa ne bayan ganawar da Gabam ya yi da El-Rufai da kuma wani jigon PDP da ake zargin shirin haɗaka ne kan zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar SDP, Alhaji Shehu Gabam, ya musanta jita-jitar yarjejeniya da jam'iyyun adawa a Najeriya.
Gabam ya ƙaryata haɗaka da dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kafin zaben 2027.
Shugaban SDP ya yaba wa Nasir El-Rufai
Gabam ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa na gidan talabijin na TVC a ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban SDP ya ce burin jam’iyyar shi ne gina tsari mai karfi da samar da madogarar da za ta ba ‘yan Najeriya zabin shugabanci mai nagarta.
Da yake magana kan ganawarsa da El-Rufai, Gabam ya bayyana shi a matsayin mutum mai tasiri wanda yake tayar da hankalin wasu ‘yan siyasa.
“Babu wata yarjejeniya da kowa, a matsayina na shugaban jam’iyya, ban taba tattaunawa kan wani shirin yarjejeniya ba."
"Mun mayar da hankali ne kan nazarin dabarunmu daga 2024 da kuma gina dandamali mai karfi domin tunkarar zabe.”
“El-Rufai mutum ne mai karfi, amma dangantakarmu na kashin kai ne, ba siyasa ba, wasu na kara wa ganawarmu nauyi don haifar da husuma da ba ta dace ba."
- Alhaji Shehu Gabam
Gabam ya musanta haɗaka da Atiku, El-Rufai
Sai dai ya nesanta jam’iyyar SDP daga duk wata alaka ta siyasa da tsohon gwamnan na Kaduna, cewar Punch.
Gabam ya yi magana kan gazawar jam’iyyun APC da PDP, ya bukaci 'yan Najeriya su nemi gaskiya da adalci daga gwamnatin Bola Tinubu.
“Gazawar PDP da APC a bayyane take, a matsayimu na SDP, muna da alhakin gina dandamali mai gaskiya wanda zai ba ‘yan Najeriya damar sararawa."
“Tsadar rayuwa ta yi muni, wasu manufofi kuma sun kara wahalar da al’ummar kasa, mutane na biyan karin kudin wuta, abinci, da sufuri, amma ana cewa tattalin arziki yana gyaruwa."
- Shehu Gabam
Gabam ya bayyana damuwarsa kan salon mulki karkashin shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa gwamnatin ta yi nisa da matsalolin da ‘yan kasa ke fuskanta.
Ya nuna tsadar rayuwa, rashin wadatar abinci, da matsalolin sufuri a matsayin kalubale da suka addabi al’umma.
Shugaban na SDP ya yi kira ga gwamnati da ta sake nazarin manufofinta, musamman wadanda suka shafi walwalar al’umma.
El-Rufai ya gana da Al-Mustapha, jigon PDP
Kun ji cewa Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gana da Manjo Hamza Al-Mustapha da shugaban jam'iyyar SDP da jigon PDP.
Rahotanni sun tabbatar da ganawar ba ta rasa nasaba da halin da kasa ke ciki da kuma shirye-shiryen jam'iyyun adawa kan zaben 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng