Kotu Ta Yi Hukuncin da Ka Iya Karya Wike, Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar PDP

Kotu Ta Yi Hukuncin da Ka Iya Karya Wike, Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar PDP

  • Kotun Ribas mai zama a Fatakwal ta tsige shugaban PDP na jihar, Hon. Chukwuemeka Aaron da sauran 'yan kwamitin gudanarwa (SWC)
  • Alkalin kotun Mai shari'a Stephen Jumbo ya yanke hukuncin cewa PDP ta saɓawa doka wajen gudanar da tarukan zaɓen shugabanni
  • Wannan dalili ne ya sa alkalin ya soke dukkan zaɓukan da PDP ta gudanar daga matakin gundumomi, kananan hukumomi da jiha

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Babbar kotun Ribas da ke zaune a Fatakwal ta yanke hukuncin tsige shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hon. Chukwuemeka Aaron.

Kotun ta kuma soke dukkan zaɓukan shugabannin PDP a matakan gundumomi, ƙananan hukumomi, da jiha da aka gudanar a watan Yulin 2024.

Umar Damagum da Nyesom Wike.
Kotu ta sauke shugaban APC na tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike a jihar Ribas Hoto: Umar Damagum, Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar PDP na Ribas

Hukuncin ya fito ne daga Mai Shari’a Stephen Jumbo, wanda ya ce zaɓukan sun saba wa tanadin doka, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hafsan tsaro ya fadi sinadarin kawo ƙarshen ta'addanci a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba jam'iyyar PDP ta gudanar da tarukan zaɓen shugabanni a Ribas a daidai lokacin da rikicin siyasar jihar ya yi tsanani.

PDP reshen Ribas ta faɗa rigima ne tun lokacin da aka samu saɓani tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da mai gidansa, Nyesom Wike, ministan Abuja na yanzu.

Hakan ya sanya aka gudanar da zaɓukan shugabannin PDP ba tare da cikakken haɗin kai ko amincewa daga duka masu ruwa da tsakin jam'iyyar ba.

Kotun ta yi wannan hukunci ne biyo bayan ƙarar da aka shigar a gabanta, inda masu ƙara suka nemi a soke tarukan zaɓen da suka gudana bisa hujjar rashin bin ka’idojin gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Kotu ta soke tarukan zaɓen shugabannin PDP

Kotun ta amince da ƙorafin masu shigar da ƙara, inda ta bayyana cewa zaɓukan sun zama marasa inganci saboda rashin bin doka da oda.

Kara karanta wannan

N40bn ta yi kadan: INEC ta fadawa majalisa biliyoyin da take so a ware mata a 2025

Wannan hukunci na zuwa ne bayan babbar kotun ta rusa zaɓukan APC mai adawa a jihar Ribas a makonnin da suka shige, rahoton Daily Trust.

Kotu ta soke zaɓukan APC a matakin gundumomi, ƙananan hukumomi, da jiha, waɗanda suka haifar da Cif Tony Okocha a matsayin shugaban jam’iyya APC na Ribas.

Wannan ya ƙara nuna tsananin rikicin siyasar da ke faruwa a manyan jam'iyyu biyu, PDP da APC a jihar Ribas.

Jam'iyyar PDP ta take umarnin kotu

A ranar 20 ga Yuli, 2024, babbar kotun jihar, ƙarƙashin Mai Shari’a Charles Wali, ta dakatar da PDP daga ci gaba da gudanar da zaɓukan.

Duk da wannan umarnin, jam’iyyar ta ci gaba da shirye-shirye har ta gudanar da tarukan zaɓen.

Dalilin haka ne babbar kotun ta yanke hukuncin soke dukkan sakamakon zaɓukan da PDP ta gudanar a zamanta na yau Litinin, 13 ga watan Janairu, 2025.

Rikici ya ƙara tsananta kan kujerar sakataren PDP

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta yi bayani a kan sace sama da N1bn daga asusun gwamnati

Kun ji cewa ga dukkan alamu akwai sauran rina a kaba dangane da rigimar da ta ɓalle a PDP kan kujerar sakataren jam'iyya na ƙasa.

Sanata Samuel Anyanwu ya shiga ofis a hedkwatar PDP ta ƙasa da ke Abuja, an ji yana cewa ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban kotun ƙolin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262