"Ba Siyasa ba ce": Dalilin da Ya Sa Gwamna Bala Ke Sukar Tsare Tsaren Bola Tinubu
- Gwamnan Bauchi ya ce babu wata ƙulalliyar siyasa da ta sa yake sukar tsare-tsaren shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- Sanata Bala Mohammed ya ce yana faɗawa shugaban gaskiya ne domin tunatar da shi nauyin da Allah ya ɗora masa na yi wa al'umma adalci
- Ya ce dole ne shugaban ƙasa ya nemi shawarwari daga masu ruwa da tsaki a duk wani tsari da yake tunanin zai amfani talakawan da yake mulka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana cewa sukar da yake wa shugaban kasa, Bola Tinubu ba ta da alaka da siyasa.
Gwamna Bala ya ce ba siyasa tasa yake sukar tsare-tsaren Tinubu ba sai dai burinsa a haɗa kan ƙasa da tabbatar da adalci ga al’ummar Najeriya.
Bala Mohammed ya faɗi haka ne da yake martani kan wani rahoto da aka jinginawa hadimin shugaban ƙasa, Sunday Dare, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Gwamna Bala na sukar Bola Tiinubu
Gwamna Bala ya jaddada cewa yana goyon bayan duk wani shiri ko tsari da zai amfani al’umma, kuma zai bayar da shawarwari kan abubuwan da ke buƙatar gyara.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar.
"Gwamna Bala ya soki kudirin haraji ne saboda ƙwarewarsa a matsayin tsohon ministan Abuja, gwamna mai ci a wa’adi na biyu da shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP.
"Ya fahimci cewa mulki mai tsari ya dogara ne kan haɗin gwiwa tare da gujewa manufofin tattalin arziki marasa tsari da ka iya jawo wa al’umma wahala.”
"Ba zai yiwu a zartar da wasu manufofin da za su yi tasiri a rayuwar al'umma ba tare da neman shawarwari ba.
"A tsarin mulkin dimokuraɗiyya, ya zama dole shugaban ƙasa ya tattauna da masu ruwa da tsaki, gina fahimtar juna, da kuma la’akari da shawarwari daban-daban.”
- Mukhtar Gidado.
Gwamnan Bauchi na son a yi adalci
Ƙauran Bauchi ya ƙara da cewa yana faɗawa shugaban kasa abin da ya hango ne ba don ƙalubalantar ikonsa ba, sai dai don ya tuna masa wajibcin gudanar da mulki cikin gaskiya da adalci..
A cewarsa, yana kallon shugaba Tinubu a matsayin jagora wanda ya sha afama da gwagwarmayar tabbatar da demokuraɗiyya har yau da ya hau kujera lamba ɗaya.
A rahoton Leadership, Gwamna Bala ya ci gaba da cewa:
“A lokacin da Shugaba Tinubu ke gwamna, ya taka rawar gani kuma ya tsaya kan gaskiya da goyon bayan manufofin da suka haɓaka demokuraɗiyya,."
"Musamman lokacin da ya tunkari shugaban ƙasa na wancan lokacin, Obasanjo don tabbatar da ‘yancin kananan hukumomi a jihar Legas."
Gwamnan Bauchi ya ba Sheikh Jingir saƙo
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya buƙaci Sheikh Sani Yajaya Jingir ya isar da koken ƴan Najeriya ga Bola Tinubu.
Shugaban ƙungiyar Izala mai hedkwata a garin Jos na ɗaya daga cikin manyan malumman da ke goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng