'Yan Majalisa Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokoki, Sun Zaɓi Mace Ta Maye Gurbinsa

'Yan Majalisa Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokoki, Sun Zaɓi Mace Ta Maye Gurbinsa

  • Mambobin Majalisar dokokin jihar Legas sun tsige kakakinsu, Rt Hon. Mudashiru Obasa daga kujerarsa ranar Litinin, 13 ga watan Janairu
  • An ruwaito cews ƴan majalisar sun sauke Obasa ne bisa zargin rashin ɗa'a da kuma amfani da ofishinsa ta hanyar da ba ta dace ba
  • Bayan haka kuma sun amince da naɗin Hon. Mojisola Meranda, mai wakiltar Apapa 1 a matsayin sabuwar shugabar Majalisar dokokin a zaman yau

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Legas - Ƴan majalisar dokokin jihar Legas sun tsige kakakin Majalisar, Rt. Hon. Mudashiru Obasa yau Litinin, 13 ga watan Janairu, 2025.

Ƴan majalisar sun ɗauki wannan mataki ne bisa zarginsa da rashin ɗa'a da kuma amfani da ofishinsa wajen saɓawa doka.

Mudashiru Obasa.
An sauke kakakin Majalisar dokokin jihar Legas, Rt. Hon. Mudashiru Obasa Hoto: Hon. Mudashiru Obasa
Asali: Facebook

Rahoton TVC News ya tabbatar da tsige kakakin majalisar dokokin Legas a shafin X ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Cire tallafin fetur ya fara haifar da sauƙi ga talakawa, cewar hadimin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mace ta zama kakakin Majalisar dokokin Legas

Bayan haka ne ƴan Majalisar suka zaɓi Hon. Mojisola Meranda mai wakiltar mazaɓar Apapa 1 a matsayin sabuwar kakakin Majalisar dokokin Legas.

Haka nan kuma ƴan majalisar sun zabi mataimakin shugaban masu rinjaye, Hon Fatai Mojeed a matsayin mataimakin kakakin majalisar dokokin.

A halin da ake ciki dai jami'an tsaro cikin shirin ko ta kwana sun mamaye harabar majalisar da kewayenta domin daƙile duk wata barazanar tsaro.

Meyasa aka tsige kakakin Majalisar dokokin?

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Obasa ya samu matsala da Gwamna Babajide Sanwo-Olu biyo bayan kalaman da ya yi kan zaben gwamnan Legas a 2027.

A watan Nuwamba, 2024 lokacin da Gwamna Sanwo-Olu ke gabatar da kasafin kudin 2025, Obasa ya jawo ce-ce-ku-ce da ya ce bai yi yarinta ko rasa gogewar da zai nemi takarar gwamna a Legas ba.

Kara karanta wannan

Aiki ja: Masu nadin sarauta sun taka wa gwamna birki kan nadin sabon sarki

Hon Obasa ya yi katobara ne a lokacin da ya bayyana cewa gaba ɗaya gwamnonin da aka yi a Legas ba su fi shi gogewa da kwarewa ba.

"Ni na sa kaina aikin haɗa jama'a amma wasu suka jirkita lamarin da cewa ina da burin neman takarar gwamna, akwai bukatar mu gaya wa mutane gaskiya, duk abin da muke yi muna ƙoƙarin gina APC ne.
"Batun neman takarar gwamna wani abu ne daban, ban kawo shi a raina ba amma duk da haka ba wai na yi yarinta ko ban da gogewar neman zama gwamna ba ne, waɗanda suka rigaye ni ba su fi ni da komai ba."

- Mudashiru Obasa.

An zargi Obasa na karkatar da wasu kuɗi

Daga baya an zargi Obasa da kashe Naira biliyan 17 wajen gina wata kofar shiga harabar majalisar, wanda ake ganin kuɗin sun yi yawa.

Ana kuma zarge shi da karkatar da kudi da ayyukan mazabu, ana ganin hakan ne ga sa aka sauke kakakin majalisar dokokin Legas.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun far wa jami'an tsaro, sun hallaka sama da 20 a jihar Katsina

Minista ya goyi bayan takarar dan Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa ministan matasa a Najeriya, Ayodele Olawande ya bayyana cewa ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu na da gogewar neman takarar gwamna.

A cewar ministan, Seyi Tinubu ya cancanci ya zama gwamnan jihar Legas idan aka duba ƙwarewa da gudummuwar da yake bayarwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262