Jami'an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar PDP bayan Rikicin Jam'iyya Ya Yi Kamari

Jami'an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar PDP bayan Rikicin Jam'iyya Ya Yi Kamari

  • 'Yan sanda sun mamaye hedikwatar jam’iyyar PDP yayin da rikicin Samuel Anyawu da Ude Okoye na zama sakataren jam'iyyar ya yi kamari
  • Rikici ya fara ne bayan kotu ta nada Okoye a matsayin sakataren PDP na ƙasa yayin da Anyawu ke ƙoƙarin dawowa ofishin jam'iyyar a matsayin sakatare
  • Kotun ɗaukaka ƙara ta ba da umarnin amincewa da Okoye, amma Anyawu ya ce ya garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin da ya dakatar da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yau Litinin, ’yan sanda sun mamaye hedikwatar PDP a Abuja yayin da ake hasashen samun rikicin shugabanci a NWC.

Ana sa ran cewa masu ikirarin zama sakatarorin jam'iyyar, Samuel Anyawu da Ude Okoye, za su fara aiki, wanda hakai zai iya jawo tashin tashina.

Kara karanta wannan

Cire tallafin fetur ya fara haifar da sauƙi ga talakawa, cewar hadimin Tinubu

Yan sanda
Yan sanda sun mamaye hedikwatar PDP a Abuja. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Channels Television ta wallafa cewa lamari ya janyo ce-ce-ku-ce da fargabar rikici tsakanin magoya bayan dukkan bangarorin a harabar hedikwatar jam’iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa Anyawu ya shiga ofishinsa cikin girmamawa tare da magoya bayansa, inda ya yi addu’a kafin ya amsa tambayoyin manema labarai.

Rikicin sakataren PDP: Daga ina ya fara?

Rikicin ya samo asali ne lokacin da Anyawu ya bar ofishin sakataren ƙasa domin takarar gwamnan Jihar Imo, inda ya sha kaye a hannun gwamna mai ci.

A lokacin da Anyawu ya yi wannan takarar, Ude Okoye ya karɓi ragamar ofishin sakataren ƙasa. Bayan Anyawu ya dawo daga Jihar Imo, Okoye ya kalubalanci dawowarsa ofishin.

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci a watan da ya gabata cewa Okoye shi ne sakataren ƙasa bisa doka, kuma kwamitin gudanarwar PDP na ƙasa ya amince da wannan hukuncin.

Martanin Anyawu kan hukuncin kotu

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Arewa sun sake bijerewa kudirin haraji, sun fadi illarsa ga talaka

Duk da wannan hukunci, Samuel Anyawu ya shaida wa manema labarai cewa ya garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin da aka yanke.

“Mun ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli, domin haka har yanzu ina riƙe da ofishina a matsayin sakataren ƙasa.”

- Samuel Anyawu

Game da sanarwar da kakakin PDP ya bayar ta ayyana Okoye a matsayin sakataren ƙasa, Anyawu ya ce wannan ra’ayi ne na mai magana da yawun jam’iyyar ba wai matsayar doka ba.

Tarin 'yan sanda a hedikwatar PDP

A yayin wannan rikici, an hango tarin jami’an tsaro na ’yan sanda a harabar hedikwatar PDP domin tabbatar da zaman lafiya.

Magoya bayan dukkan bangarorin biyu sun kasance a wurin domin nuna goyon baya ga jagoransu, yayin da wasu ke fargabar barkewar rikici tsakanin bangarorin biyu.

Manyan PDP suna so a zauna lafiya

Wannan rikici ya janyo damuwa tsakanin shugabannin PDP, inda ake kiran bangarorin biyu da su sassauta matsayinsu da kuma mutunta dokokin jam’iyyar da na kasa.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya yi ridda zuwa bautar gargajiya bayan karatun boko mai zurfi

Hukumar gudanarwar PDP ta bayyana cewa tana martaba hukuncin kotu kuma tana fatan samun maslaha mai dorewa tsakanin bangarorin biyu.

PDP ta ce ta shirya tunkarar 2027

A wani rahoton, kun ji cewa ja m'iyyar PDP ta ce tana shiri domin kwace mulki daga hannun APC a zaben shugaban kasa na 2027.

Jam'iyyar PDP ta ce a shirye take domin magance rikice rikicen cikin gida da take fuskanta wanda suka kawo mata cikas a 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng