'PDP za Ta Kwace Mulki a Hannun APC a Zaben 2027,' Sakataren Jam'iyya

'PDP za Ta Kwace Mulki a Hannun APC a Zaben 2027,' Sakataren Jam'iyya

  • Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta gyara kuskuren da ta yi a zaɓen 2023 domin ta sake karɓe mulki daga hannun APC a shekarar 2027
  • Babban Sakataren PDP na Ƙasa, Samuel Anyanwu, ya ce babu wata baraka a jam’iyyar kuma sun shirya tsaf domin kalubalantar APC
  • Anyanwu ya tabbatar da matsayinsa a matsayin sakataren PDP duk da hukuncin kotu, yana mai cewa za a jira hukuncin ƙarshe daga Kotun Ƙoli

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tana kan hanya domin gyara kurakuren da ta yi a zaɓen 2023 tare da tabbatar da cewa ta sake karɓe mulkin ƙasa a shekarar 2027.

Babban Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai, inda ya jaddada cewa PDP na kan turbar samun nasara a gaba.

Kara karanta wannan

Tun kafin 2027, PDP ta haramta wa kowa neman takara, ta tsayar da gwamna ba hamayya

Damagun
PDP ta fara shirin tunkarar 2027. Hoto: PDP Official
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa Sanata Anyanwu ya ce jam'iyyar tana kan aiwatar da shirye-shiryenta domin sake zama babbar jam’iyyar siyasa a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP: Batun gyara kuskuren zaɓen 2023

Sanata Anyanwu ya bayyana cewa PDP ta koyi darussa daga zaɓen 2023, kuma yanzu ta shirya tsaf domin sake fafatawa a 2027.

Sakataren jam'iyyar ya ce;

“Mun yi kuskure a zaɓen 2023, amma abin da ya fi muhimmanci gare mu shi ne mu sake karɓe shugabancin ƙasa a 2027.
"Wannan shi ne burinmu kuma muna kan aiki domin ganin mun cimma hakan.”

Ya kuma bayyana cewa PDP ta gudanar da tarukanta a jihohi 29 ba tare da wata matsala mai tsanani ba, sai wasu ‘yan ƙananan matsaloli da ya ce ba sabon abu ba ne a kowace jam’iyya.

Matsayin Anyanwu bayan hukuncin kotu

Sanata Anyanwu ya yi karin bayani kan matsayinsa a PDP, yana mai cewa har yanzu shi ne sakatare na ƙasa duk da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ya cire shi.

Kara karanta wannan

Yadda zargin Peter Obi ya jefa rayuwarmu a cikin barazana," Kakakin APC

Ya ce;

“Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara bai cire ni daga matsayin sakataren PDP ba saboda har yanzu muna da shari’a a Kotun Ƙoli.
"Kuma akwai hukuncin Kotun Tarayya da ya tabbatar da rashin kawo karshen wa’adin aikina.”

Sanata Anyanwu ya jaddada cewa zai ci gaba da rike matsayin sa har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ƙarshe kan lamarin.

Rikicin jam’iyyar PDP da alaƙa da Wike

Sanata Anyanwu ya musanta zargin cewa akwai tsagi da ya balle a cikin PDP, yana mai cewa jam’iyyar daya ce karkashin cikakken shugabancin Umar Damagum.

Ya kuma bayyana cewa yana da kyakkyawar alaƙa da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tun lokacin da suka yi aiki tare a matsayin shugabannin ƙananan hukumomi.

“Idan akwai wata matsala da Wike, to za a magance ta ta hanyar Kwamitin Ladabtarwa na PDP. Duk wani lamari dole ne ya bi tsarin jam’iyya.”

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi wa APC martani mai zafi kan shirin karbe Kano a 2027

- Sanata Anyanwu

PDP ta yi kira ga mabiyanta a Najeriya

PDP ta yi kira ga magoya bayanta su ci gaba da bai wa jam’iyyar goyon baya, tana mai tabbatar da cewa za ta sake farfaɗowa domin sake jan ragamar mulkin ƙasa a 2027.

Sanata Anyanwu ya ce,

“PDP tana nan a tsaye, kuma muna ci gaba da aiki tukuru domin ganin mun dawo da martabar jam’iyyar. Zaɓen 2027 zai zama wani sabon babi a tarihin PDP.”

An fara shirin kayar da Tinubu a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan siyasa da wasu 'yan jam'iyyar adawa sun fara wasu shirye shirye domin tunkarar zaben 2027.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau na cikin wadanda suka fara neman hada tafiyar siyasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng