Da Gaske Osinbajo Ya bar Jam'iyyar APC? an Bayyana Gaskiya kan Rade Radin

Da Gaske Osinbajo Ya bar Jam'iyyar APC? an Bayyana Gaskiya kan Rade Radin

  • Kakakin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Laolu Akande, ya yi magana kan jita-jitar cewa mai gidansa ya bar APC
  • Akande ya musanta labarin inda ya bayyana cewa Osinbajo bai bar siyasa ko jam'iyyar APC ba yana nan daram
  • Mataimakin Osinbajo ya ce babu wani abu da ya nuna Osinbajo ya janye daga APC, duk da yake bai shahara a harkokin siyasa ba
  • Wasu na ganin shan kayen Osinbajo a zaben fitar da gwanin APC ya sa ya rage shiga harkokin siyasa yayin da wasu cewa samun muƙaminsa ne sila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kakakin tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Laolu Akande ya magantu kan rade-radin cewa mai gidansa ya bar siyasa.

Akande ya ce babu dalilin da zai sa a yi tunanin Osinbajo ya bar siyasa ko kuma ya fita daga jam'iyyar APC da aka gudanar a shekarar 2022 a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Fadan kabilanci ya yi sanadin rasa rayukan mutane 11 a Jigawa, an fadi silar rikicin

Hadimin Osinbajo ya magantu kan ficewar mai gidansa daga APC
Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya musanta cewa mai gidansa ya bar APC. Hoto: Professor Yemi Osinbajo.
Asali: Twitter

Yadda Osinbajo ya rasa rikiti a APC

Akande ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a Legas ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun bayan barinsa ofis a 2023, Osinbajo bai yawaita shiga harkokin siyasa ba, abin da ya haifar da jita-jitar cewa ya bar APC da siyasa baki daya.

Osinbajo ya shiga zaben fitar da gwani na APC a 2022, amma bai samu tikitin jam’iyyar ba, inda ya sha kaye a hannun Bola Tinubu.

Osinbajo ya taba zama Kwamishinan Shari’a da Antoni-janar na jihar Legas daga 1999 zuwa 2007, a karkashin mulkin Bola Tinubu a matsayin gwamna.

Wasu masu lura da siyasa suna ganin shan kayen Osinbajo a zaben fitar da gwani ya sa ya rage shiga harkokin siyasa, yayin da wasu ke danganta hakan da nadinsa a matsayin mai ba da shawara a hukumar GEAPP.

An ƙaryata rade-radin barin Osinbajo APC

Kara karanta wannan

'Dan majalisar NNPP, ya fadi abin da Ganduje ya 'shiryawa' jam'iyyar APC a 2027

Da aka tambayi Akande game da rayuwar siyasar tsohon shugabansa, ya ce ba zai sa shi cikin maganarsa ba, amma a saninsa Osinbajo bai bar siyasa ba.

Akande ya kara da cewa, idan aka gayyaci Osinbajo zuwa wani taron jam’iyyar APC mai muhimmanci, babu shakka zai halarta, Daily Post ta ruwaito.

"Ba na son sa tsohon shugaban cikin maganata, amma babu dalilin cewa ya fita daga APC; har yanzu yana cikin jam’iyyar."

- Laolu Akande

An gano yadda Tinubu ya yi wa Buhari wayo

Kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Babafemi Ojudu ya bayyana yadda Bola Tinubu ya yi wa Muhammadu Buhari dabara a zaben fitar da gwani na APC.

Sanata Ojudu ya ce Tinubu ya shammaci Buhari a wajen neman tikitin takara a zaben fidar da gwani na APC a 2022 da suka fafata da Farfesa Yemi Osinbajo a Abuja.

Dan siyasar ya ce Buhari bai goyi bayan Osinbajo ko Tinubu ba a zaben fitar da gwani inda ya ana hasashen ya so Ahmad Kadan wanda hakan ya shafi sakamakon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.