'Ya Cancanta': Ana Hasashe Ɗan Tinubu Zai Nemi Takara, Minista Ya Goya Masa Baya

'Ya Cancanta': Ana Hasashe Ɗan Tinubu Zai Nemi Takara, Minista Ya Goya Masa Baya

  • Ministan Matasa a Najeriya, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa Seyi Tinubu ya cancanci zama Gwamnan Lagos saboda kwarewarsa da irin gudunmawar da ya bayar
  • Olawande ya ce Seyi ya na da jajircewar aiki, yana goyon bayan matasa kuma yana son ganin ci gaban su a Najeriya
  • A watan Nuwamba 2024, kungiyar matasa ta CONYL ta amince da Seyi Tinubu ya gaji Gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin gwamna jihar na gaba
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu na sukar maganar goyon bayan Seyi Tinubu kan takarar gwamna inda suke cewa ba gadon gidansu ba ne

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ikeja, Lagos - Ministan Matasa, Ayodele Olawande ya yi magana kan hasashen cewa Seyi Tinubu zai tsaya takarar gwamnaa Lagos.

Ministan ya ce Seyi Tinubu wanda ɗa ne Shugaba Bola Tinubu, ya cancanci zama gwamnan Legas saboda shekarun sun kai ya yi hakan.

Kara karanta wannan

Abin na gida ne: Kanin tsohon gwamna ya shirya neman kujerar yayansa da ya bari

Minista ya goyi bayan ɗan Tinubu ya nemi gwamnan Lagos
Ministan matasa ya goya wa ɗan Bola Tinubu baya a nemi takara. Hoto: Seyi Tinubu.
Asali: Twitter

An goyi bayan dan Tinubu ya nemi gwamna

Ministan ya bayyana hakan yayin wata hira da Seun Okinbaloye, inda ya ce Seyi shugabansa ne kuma yana da ƙarfin jagorantar jihar Lagos, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Nuwamba 2024, kungiyar matasa ta CONYL ta amince da Seyi Tinubu ya gaji Gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin gwamnan jihar.

CONYL ta ce akwai buƙatar dan shugaban ƙasa, Bola Tinubu watau Seyi Tinubu ya nemi kujerar da babansa ya hau a kakar zabe ta 2027.

Kungiyoyin matasan da suka fito daga shiyyoyi shida na kasar nan sun bayyana dalilinsu na sha'awar Seyi Tinubu ya zama gwamnan Lagos.

PDP ta caccaki masu zuga Seyi Tinubu

Sai dai hakan ya samu tasgaro inda jam'iyyar PDP reshen jihar ta caccaki masu neman haka da cewa kujerar ba gadon gidansu ba ne.

Kakakin jam'iyyar, Hakeem Amode Amode ya yi fatali da kiraye-kirayen inda ya ce Lagos ba za su taba goyawa mahaifinsa da kuma shi kansa Seyi Tinubu baya ba.

Kara karanta wannan

"Mun gamsu da kai": Gwamna a Arewa ya samu goyon bayan takara a zaɓen 2027

Ya caccaki masu neman mayar da mulkin Lagos ta iyalai inda ya ce hakan zai fuskanci turjiya mai tsanani daga wurinsu, Vanguard ta ruwaito.

Takarar gwamna: Minista ya goyi bayan ɗan Tinubu

Ministan matasa, Olawande ya ce Seyi matashi ne mai tarbiyya da ya tallafa wa matasa da dama, tun kafin mahaifinsa ya zama shugaban ƙasa.

"Shekarunsa ba su kadan ba, yana da damar zama gwamna, yana tallafa wa matasa kuma yana kokarin ganin sun samu ci gaba mai ma’ana.”

- Ayodele Olawande

Ministan ya ƙara da cewa Seyi bai bar Najeriya don jin daɗin rayuwa ba, yana nan yana aiki don ganin an inganta rayuwar matasa a ƙasar.

Seyi Tinubu ya ba yan Najeriya hakuri

A baya, kun ji cewa daya daga cikin 'ya'yan Shugaba Bola Tinubu, Seyi Tinubu ya bayyana cewa ya na da tabbacin shugaban ba zai ba da kunya ba.

Seyi ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya ce irin shugaban da 'yan kasar ke muradi ya zo a wannan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.