Sanatan APC Ya Kassara Jam'iyyun Adawa, Mutane 8,000 Sun Dawo Jam'iyyarsa

Sanatan APC Ya Kassara Jam'iyyun Adawa, Mutane 8,000 Sun Dawo Jam'iyyarsa

  • Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta samu karuwa a jihar Abia bayan dubban mutane sun sauya sheka zuwa cikinta
  • Sanata Orji Uzor Kalu ya tarbi mutane sama da 8,000 da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga sauran jam'iyyun siyasa a jihar
  • Kalu ya ce ya na aiki dare da rana don tabbatar da zaman lafiya a APC da kuma shirin lashe zaben gwamna na 2027 a jihar
  • Shugaban APC na jihar Abia ya ce jam'iyyar ta shirya karɓar mulki a 2027, tare da alkawarin kawo karin romon dimokuradiyya ga jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Umuahia, Abia - Sanata mai wakiltar yankin Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya tarbi sama da mutane 8,000 da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin Najeriya sun tarfa ƴan bindiga, sun hallaka sama da 100

An gudanar da taron ne a ranar Juma'a 10 ga watan Janairun 2025 inda al'umma daga sauran jam'iyyun siyasa suka koma APC.

Yan jam'iyyun adawa 8,000 sun koma APC
Sanata Orji Uzoh Kalu ya karbi yan adawa 8,000 zuwa APC a Abia. Senator Orji Uzoh Kalu.
Asali: Facebook

Sanata ya sha alwashin kwace mulki a Abia

Da yake magana yayin karɓar masu sauya shekar Sanata Kalu ya ce suna ta kokarin ganin sun kwace mulki a hannun LP, cewar The Sun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalu ya bayyana cewa yana aiki dare da rana don tabbatar da zaman lafiya a APC a jihar, tare da nufin lashe zaben gwamna a 2027.

Sanata Kalu ya nuna farin cikin cewa kokarinsa ya fara haifar da ɗa mai ido, wanda hakan ya kawo yawan masu sauya shekar zuwa APC duk da cewa jam’iyyar ba ta kan mulki.

Sanata ya nuna farin ciki kan bunƙasar APC

Sanatan ya ce abin farin ciki ne ganin mutum kamar Onumah da wasu daga Abiriba sun shiga APC, yana mai cewa wannan ci gaba zai tabbatar da cewa Abia ta Arewa da gaba ɗaya jihar sun zama APC.

Kara karanta wannan

'Ko a jikinmu': Gwamnan APC kan hadakar jam'iyyun adawa, ya fadi dabarbarun da za su yi

Tsohon gwamnan ya ce babu shakka Chief Onumah, wanda ya samu nasara sosai a harkar kasuwanci, ya taimaki mutane da dama a matsayinsa na ɗan kasuwa, amma yana bukatar shiga gwamnati don taimaka wa mutanensa fiye da haka.

"Onumah babu shakka ya yi nasara sosai a kasuwanci, ya taimaki mutane a matsayin ɗan kasuwa, ban ga wanda ba zai goyi bayansa ba a APC."
"Dole mu kasance a gwamnati don taimaka wa mutanenmu fiye da yadda muke, kuma hakan za a yi ta hanyar APC, wacce babbar jam’iyya ce a Afrika."

- Orji Uzoh Kalu

Kalu ya shawarci magoya bayan APC

Kalu ya ja hankalin sabbin mambobin da su kawo karin mutane cikin jam’iyyar don tabbatar da nasarar lashe zaben gwamna a 2027, Daily Post ta ruwaito.

Shugaban APC na jihar Abia, Kingsley Ononogbu, ya ce jam’iyyar za ta karɓi mulki a 2027, tare da yi wa mutanen Abia alkawarin karin romon dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Ganduje da APC sun yi babban kamu, tsohon shugaban PDP ya koma jam'iyya

Babban jigon PDP ya koma APC

Kun ji cewa jam'iyyar APC ta ƙara samun ƙaruwa a jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya bayan sauya sheƙar tsohon shugaban PDP.

Wani ƙusa a PDP kuma fitaccen ɗan kasuwa a Abia, Cif Kelvin Jumbo Onumah ya jagoranci dubannin magoya bayansa, sun koma jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.