Tinubu Ya Sake Gamo da Matsala, Tsofaffin Shugabannin Kasa Sun Shiga Tafiyar Shekarau

Tinubu Ya Sake Gamo da Matsala, Tsofaffin Shugabannin Kasa Sun Shiga Tafiyar Shekarau

  • Tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, yana jagorantar manyan Arewa wajen tattaunawa da shugabannin Kudu don kulla kawance gabanin zaben 2027
  • A cewar rahotanni, tsofaffin shugabannin kasa, Olusegun Obasanjo da Janar Yakubu Gowon suna daga cikin masu mara wa wannan tafiyar baya
  • Shekarau da kungiyarsa, League of Northern Democrats, sun fara tattaunawa da shugabannin siyasa daga Kudu don kafa tafiyar siyasa mai karfi da hadin kai
  • Wannan na zuwa ne yayin da wasu jam'iyyun adawa a Najeriya ke shirin yin haɗaka mai ƙarfi domin tunkarar zaben 2027 da Bola Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, na ci gaba da jagorantar manyan Arewa wajen tattaunawa da manyan shugabannin Kudu domin kafa kawance kafin zaben 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware biliyoyin Naira kan jiragen shugaban kasa a 2025

Majiyoyi sun bayyana cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da kuma Janar Yakubu Gowon suna daga cikin masu goyon bayan wannan kungiyar.

Tafiyar siyasar Shekaru ta kara samun karfi domin kifar da Tinubu
Tsofaffin shugabannin kasa sun mara wa tafiyar Ibrahim Shekarau baya domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu. Hoto: Mallam Ibrahim Shekarau, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Ana shirin sauyawa tafiyar Shekarau suna

Rahoton Punch ya ce Shekarau, wanda ke jagorantar kungiyar League of Northern Democrats ya shiga tattaunawa da shugabannin siyasa daga Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas, da Kudu maso Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar LND, Dokta Umar Ardo, ya bayyana a ranar 5 ga Janairun 2025 cewa kungiyar za ta rikide zuwa jam’iyyar siyasa saboda bukatar kafa tafiyar siyasa ta kasa mai nagarta.

A cewarsa, LND na shirin rikidewa zuwa League of National Democrats domin samar da zabin shugabanci mai nagarta ga 'yan Najeriya.

“Wannan sabuwar tafiya ta siyasa za ta samar da zabi na gaske ta hanyar tabbatar da cancanta, inganta gaskiya, da samar da shugabanni masu kwarewa da nagarta."

- Umar Ardo

Obasanjo da Gowon sun ba da shawara

Kara karanta wannan

El-Rufai, Shekarau da 'yan siyasan da za su iya yakar APC da Tinubu a 2027

Rahotanni sun ce Obasanjo da Gowon sun shawarci shugabannin kungiyar su mai da ita ta kasa baki daya tare da haɗa shugabannin kudu.

Obasanjo ya bukaci LND a karshen Oktobar 2024 da su sake suna zuwa National League of Democrats saboda manufofin da kungiyar ke goyan baya sun shafi kasa baki daya.

Tsohon shugaban kasa ya karbi bakuncin tawagar wakilai 20 na LND karkashin jagorancin Shekarau a gidansa da ke Abeokuta, inda ya ce ba zai ki zama mai ba su shawara ba.

“Lokaci ya yi da za mu fara aiki don muradin kasa, Eh, kun kira kanku League of Northern Democrats, amma ina fatan ku kira kanku National League of Democrats domin inda kuka fito bai kamata ya zama matsala ba."

- Olusegun Obasanjo

Shekarau ya magantu kan tafiyar siyasarsu

Kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya nuna cewa sabuwar tafiyarsu na son zaburar da jama'a kan shugabanci na gari a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban Ghana ya jefa mutanen duniya a mamaki wajen kiran Tinubu a taro

Tsohon gwamnan ya fadi haka ne bayan ziyarar da ya kai Abeokuta domin zama da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo domin gabatar masa kudirin ƙungiyar.

Malam Ibrahim Shekarau ya ce kasar nan, musamman Arewa da su ka fito na fama da matsaloli da ke bukatar a magance su cikin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.